Da Dumi-Dumi: Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Fado a Jihar Legas

Da Dumi-Dumi: Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Fado a Jihar Legas

  • An samu hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a birnin Ikeja, babban birnin jijar Legas dake yankin Kudu maso Yamma
  • Jirgin saman ya faɗo ne dai a yankin wasu gine-gine da tsakar ranar Talata, 1 ga watan Agustan 2023
  • Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa sun samu nasarar ceto mutum biyu dake cikin jirgin da ya yi hatsarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya auka kan wasu gine-gine a birnin Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Jirgin saman ya kama da wuta a kusa da tashar filin tashi da saukar jiragen sama ta Murtala Muhammad, inda jirgin yake kan hanyar zuwa, cewar rahoton Daily Trust.

Jirgin sama ya yi hatsari a Legas
Jirgin saman ya fado ne kan gine-gine Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Jirgin saman mai saukar ungulun dai ya faɗo ne a yankin Oba Akran na birnin Legas inda ya kama da wuta.

Kara karanta wannan

Hadi Sirika Ya Bayyana Halin Da Mutanen Da Suka Yi Hadari a Jirgi Mai Saukar Ungulu a Legas Ke Ciki

Kakakin hukumar bincike ta NSIB, Tunji Oketunbi, ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin saman na ranar Talata da rana, rahoton Channels Tv ya tabbatar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka kuma wani jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas, (LASEMA), ya bayyana cewa jirgin ya kama da wuta lokacin da lamarin ya auku.

A nata ɓangaren, hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa mutum biyu ne a cikin jirgin saman mai saukar ungulu lokacin da ya yi hatsari.

Kodinetan hukumar NEMA na yankin Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, a dandalin hukumar na WhatsApp, ya ce duk da dai ba a san mai jirgin ba, dukkanin mutum biyun dake cikin jirgin an ceto su da ransu.

Jami'an hukumomin NEMA, LASEMA da NSIB duk sun hallara inda hatsarin ya auku.

Ga bidiyon yadda hatsarin jirgin ya auku nan ƙasa:

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Gwamnati Ta Lalata Shaguna Da Matsunan Hausawa a Jihar Kudu

Hatsarin jirgin saman na ranar Talata, na zuwa ne shekara uku bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakin kamfanin Quorom Aviation, ya faɗo a yankin Opebi na jihar Legas, a watan Agustan 2020.

Jirgin Sojin Sama Ya Yi Hatsari

A wani labarin na daban kuma, jirgin sojin sama ya yi hatsari a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Matuƙan jirgin horar da sojojin saman na FT-7NI sun tsira a hatsarin da ya auku, yayin da aka kafa kwamitin bincike domin gano abinda ya haddasa hatsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel