Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Sabon Rabon Tallafin Da Mutum 1.8m Za Su Amfana

Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Sabon Rabon Tallafin Da Mutum 1.8m Za Su Amfana

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shirya faranta ran masu ƙaramin ƙarfi mutum 1.8m a jihar
  • Gwamna Zulum ya ƙaddamar da sabon rabon tallafi wanda iyalai 300,000 za su amfana da shi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta rage wahalhalun da al'umma su ke sha

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da sabon rabon tallafi wanda zai amfani iyalai 300,000 akan mutum shida kowane gida wanda zai kai ga mabuƙata mutum 1.8m.

Zulum ya ƙaddamar da rabon ne a sansanin ƴan gudun hijira na Muna a ƙaramar hukumar Lere, ranar Talata 1 ga watan Yulin 2023. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Ku Rage Zafi: Gwamnan APC a Arewa Ya Bada Umarnin A Bai Wa Kowane Ɗalibin Jiharsa Tallafin N10,000

Gwamna Zulum ya kaddamar da sabon rabon tallafi
Mutum 1.8m ne za su amfana da sabon rabon tallafin Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi bayanin cewa jihar Borno ta fara rabon tallafin ne wata ɗaya da ya gabata, inda take ƙara ci gaba da rabon domin ganin an magance matsalar abinci.

Gwamna Zulum ya kuma yi nuni da cewa rabon tallafin na farko an gudanar da shi ne a Gwoza da wasu ƙauyuka guda uku a ƙaramar hukumar Kukawa da suka haɗa da Baga, Cross Kauwa da Doron Baga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda tsarin sabon rabon tallafin yake

Gwamnan ya ƙara da cewa shirin rabon tallafin an yi shi ne domin rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haifar.

A ƙarƙashin tsarin, duk wanda ya cancanci samun tallafin, yana samun tsabar kuɗi N5,000, buhun shinkafa, buhun wake da atamfa guda ɗaya (ga mata).

Zulum ya yi nuna da cewa gwamnatinsa za ta ba jindaɗi da walwalar al'ummar jihar muhimmanci domin tabbatar da cewa an yi dukkanin abubuwan da suka dace domin rage wahalhalun da su ke sha.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa

Gwamnan ya kuma buƙaci al'ummar jihar da su ba gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya, inda ya bayyana cewa wahalar da ake sha a dalilin cire tallafin man fetur ba mai ɗorewa ba ce.

Zulum Ya Rabawa Magidanta Kayan Abinci

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ƴa faranta ran magidanta 13,000 a jihar.

Gwamnan ya yi magidantan rabon kayan abinci domin tallafa musu bisa halin da rikicin da ake a jihar ya jefa su a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel