An Shiga Duhu a Nijar Bayan Najeriya Ta Katse Wutar Lantarkin Da Take Ba Kasar

An Shiga Duhu a Nijar Bayan Najeriya Ta Katse Wutar Lantarkin Da Take Ba Kasar

  • A ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023, wasu birane a Jamhuriyar Nijar sun rasa wutar lantarki a dalilin juyin mulkin da aka yi a ƙasar satin da ya gabata
  • Mazauna biranen Yamai, Maradi da Zindar duk sun fuskanci rashin wutar lantarki wacce ta kai ta tsawon sa'o'i biyar
  • Nigelec, amfanin wutar lantarki na ƙasar, ya tabbatar da aukuwar lamarim inda ya yi nuni da cewa rashin wutar lantarkin ya auku a dalilin yanke wutar da Najeriya take ba wa ƙasar ne

A wani mataki na ƙara matsin lamba kan sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, Najeriya ta katse wutar lantarkin da take ba wa Jamhuriyar Nijar.

Wannan katse wutar dai da Najeriya ta yi wa makwabciyarta, ya sanya manyan birane a Jamhuriyar Nijar shiga cikin duhu, cewar rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Ya Ja Kunnen Gwamnatin Tinubu Kan Hambarar da Bazoum a Nijar

Najeriya ta sanya Nijar cikin duhu
Najeriya ta sanya Jamhuriyar Nijar cikin duhu Hoto: General Abdourahmane Tchiani (@AfricanHub_), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jamhuriyar Nijar dai ta fi dogaro ga Najeriya wajen samun wutar lantarki. Katse wutar ya sanya an shiga duhu a babban birnin Jamhuriyar Nijar wato Yamai, rahoton BBC News ya tabbatar.

Biranen Nijar da dama sun shiga duhu

Haka kuma matsalar rashin wutar lantarkin ta shafin manyan birane irin su Zindar da Maradi, biranen da ba a saba da ɗauke musu wutar lantarki ba, saɓanin ƙasar dake samar musu da wutar lantarkin wato Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya tilasta kamfanin wutar lantarki na Nijar (Nigelec) komawa yin amfani da tsarin karɓa-karɓa wajen rarraba wutar lantarkin a tsakanin biranen ƙasar.

Kamfanin Nigelec ya ɗora alhakin matsalar wutar lantarkin kan katse musu wuta da Najeriya ta yi, wanda hakan ya sanya kamfanin ya koma ba wasu wuraren wutar lantarki ta sa'a ɗaya sannan a ɗauke sai bayan kusan sa'o'i biyar sai a sake dawo musu da wutar lantarkin.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

Duk da dai, babu wata sanarwa a hukumance daga Najeriya kan katse wutar lantarkin da take ba Jamhuriyar Nijar, matakin na zuwa ne a cikin takunkumin da aka ƙaƙaba kan sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar.

Ministan Buhari Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Nijar

A wani labarin kuma, minista tsohon shugaban ƙasa Muhammaɗu Buhari, ya ka kennen gwamnatin Shugaba Tinubu kan yin amfani da ƙarfin soja a Nijar.

Janar Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa rikici na ɓalle wa a Nijar, ƙasar nan za ta shiga cikin gagarumar matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel