Juyin Mulkin Nijar Vs ECOWAS: Shugaba Tinubu Ya Samu Sabon Gargadi

Juyin Mulkin Nijar Vs ECOWAS: Shugaba Tinubu Ya Samu Sabon Gargadi

  • An gargaɗi Shugaba Bola Tinubu da kada ya jagoranci ƙungiyar ECOWAS ɗaukar matakin ƙarfin soja akan sojojin da suka hamɓarar da mulki a Jamhuriyar Nijar
  • Babban lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, ya bayyana cewa dakatar da Nijar daga ƙungiyar ECOWAS bai yi tsauri ba sosai
  • Ya bayyana cewa yana da kyau ƙungiyar ta ƙara sanya sabbin takunkumi kan Nijar amma kada ta yi amfani da ƙarfin soja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikeja, jihar Legas - An gargaɗi shugaban ƙasa Bola Tinubu akan yin amfani da ƙarfin soja akan sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar.

Babban lauya kuma ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, shi ne ya yi wannan kiran ga Shugaba Tinubu da sauran shugbannin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Talata, 2 ga watan Agusta, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Kwadago Ta Dakatar Da Gudanar Da Zanga-Zanga? Gaskiya Ta Bayyana

An gargadi Tinubu da ECOWAS kan Jamhuriyar Nijar
Falana ya gargadi Tinubu kada ya jagoranci ECOWAS yin amfani da karfin soja a Nijar Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Falana ya shawarci Tinubu da ECOWAS kada su yi amfani da ƙarfin soja

Falana ya buƙaci ƙungiyar ECOWAS ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, da ta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ƙara sanya takunkumi masu tsauri akan Nijar da samar da hanyoyin da za a tabbatar sun yi aiki, musamman duba da yadda sojojin suka tubure ba za su bar kan mulki ba."

Gargaɗin na lauyan na zuwa ne kwanaki biyu bayan ƙungiyar ECOWAS ta hana zirga-zirgar jirage a sararin samaniyar Nijar, inda ta ƙara da cewa ta ba sojojin wa'adin mako guda su mayar da mulki zuwa hannun farar hula.

Ta yi gargaɗin cewa za ta iya yin amfani da ƙarfin soja akan sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Ƙungiyar ta ECOWAS ta buƙaci sojojin da su gaggauta sakin Bazoum tare da mayar da shi kan muƙaminsa, wanda su ke ci gaba da tsarewa tun ranar Laraba, 26 ga watan Yuli

Kara karanta wannan

2023: Daga Ƙarshe, Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Peter Obi Ya Kalubalanci Zaɓen Tinubu

A yayin da yake magana kan matakin na ƙungiyar, Falana ya bayyana cewa dakatar da Nijar daga ECOWAS ya yi kaɗan, inda ya ƙara da cewa takunkumi mai tsauri za a ƙaƙabawa sojojin, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Idan za a iya tunawa dai, a farkon watan Yuli ne aka zaɓi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar ECOWAS.

Sojojin Nijar Sun Yi Fatali Da Matsayar ECOWAS

A wani labarin kuma, sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin farar hula a Nojar sun yi watsi da buƙatar ECOWAS ta su bar kan madafun ikon ƙasar.

Sojojin sun kuma gargaɗi ƙungiyar da kada ta kuskura ta yi amfani da ƙarfin soja akan su domin a shirye su ke su kare ƙasarsu ta haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel