Manyan Labarai A Yau
Wata budurwa ƴar Najeriya ta samu kanta cikin wani mawuyacin hali, bayan an wawushe mata makuɗan kuɗaɗe a asusun ajiyarta na banki. Ta rasa miliyoyin kuɗi.
An shiga jimami kan rasuwar Farfesa Oladele Orimoogunje na jami'ar jihar Legas (UNILAG). Shugabannin jami'ar su ne suka sanar da rasuwar Farfesan a hukumance.
Am sake samun tangarɗa dangane da shari'ar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yayin da ba a ambato shari'arsa ba yau a kotu.
Fasto William Folorunso Kumuyi, shugaban cocin Deeper Christian Life Ministry, ya bayyana abinda ubangiji ya gaya masa a kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rikicin shugabanci ya ɓarke a tsakanin ƴan bindiga domin neman karɓe ikon wasu ƙauyuka jihar Benue. A yayin rikicin rayukan ƴan bindiga masu yawa sun salwanta.
Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja a Najeriya, Abdulsalami Abubakar ya yi magana kan yadda tattaunawarsu ta kaya da sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.
Wata budurwa ta koka kan yadda soyayya ta ki zuwa gareta duk da cewa shekarunta sun kai a ce tana da samari. Ta nuna matuƙar damuwarta kan halin da take ciki.
Jami'an rundunar yan sanda a Bauchi sun kama wata matar aure kan zargin kashe jinjirin kishiyarta mai kwanaki hudu a duniya da taimakon maganin kashe kwari.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sabon saƙo ga sabbin ministocin da ya rantsar a ranar Litinin, ciki har da Nyesom Wike da sauran minitocin su 44
Manyan Labarai A Yau
Samu kari