Rashin Tausayi: Matar Aure A Bauchi Ta Kashe Jinjirin Kishiyarta

Rashin Tausayi: Matar Aure A Bauchi Ta Kashe Jinjirin Kishiyarta

  • Jami'an yan sanda a jihar Bauchi sun cika hannu da wata matar aure mara tausayi da tsoron Allah
  • Furera Abubakar ta kashe jinjirin kishiyarta kwanaki hudu bayan haihuwarsa a ranar 19 ga watan Agusta
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar ya ce ta yayyafawa jinjirin maganin kashe kwari a cibiyarsa lamarin da ya daburta lafiyarsa har ya ce ga garinku

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun kama wata matar aure mai shekaru 24 kan zargin kashe jinjirin kishiyarta mai kwanaki hudu a duniya da maganin kashe kwari.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana haka a cikin wata sanrwa da ya fitar kuma aka gabatarwa manema labarai a jihar a ranar Talata, 22 ga watan Agusta, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Aike da Muhimmin Sako Mai Jan Hankali Ga Shugaba Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

Yan sandan Bauchi sun kama matar da ta kashe jinjirin kishiyarta
Rashin Tausayi: Matar Aure A Bauchi Ta Kashe Jinjirin Kishiyarta Hoto: Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

An tattaro cewa al’amarin ya afku ne a kauyen Bantu da ke karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Yadda matar aure ta kashe jinjirin kishiyarta da maganin kashe kwari a Bauchi

Wakil ya bayyana cewa an haifi jinjirin a ranar 15 ga watan Agustan 2023 amma wacce ake zargin ta kashe shi ne a ranar 19 ga watan Agusta tun ma ba a kai ga yin taron sunansa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa Furera Abubakar ta shiga dakin kishiyar tata da maganin kashe kwari sannan ta shafa wa jinjirin lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa ba zato ba tsammani.

Kakakin yan sandan ya ce:

“Jami’an da ke aiki da rundunar yan sandan jihar Bauchi sun kama Furera Abubakar, mace mai shekaru 24 ta kauyen Bantu, karamar hukumar Ningi na jihar Bauchi kan aikata laifin kisan kai.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Ministoci 9 da Zasu Fayyace Nasarar Shugaba Tinubu Ko Gazawa da Dalilai

"An kai rahoton lamarin ga hedkwatar yan sandan Ningi a ranar 19 ga watan Agustan 2023, wanda ya bayyana cewa an haifi jinjirin kwana hudun a ranar 15 ga watan Agustan 2023 kuma wacce ake zargin, Furera Abubakar ta kashe shi a ranar 19 ga watan Agustan 2023 kafin taron suna.
“Binciken farko ya bayyana cewa wacce ake zargin kishiyar mai jegon da aka kashewa jariri ce.
“Wacce ake zargin ta shiga dakin kishiyar da maganin kashe kwari (Gramalin) sannan ta shafa shi a cibiyar jinjirin da bai warke ba.
“Maganin wanda ake zargin yana da illa, kuma shine yay i sanadiyar tabarbarewar lafiyar jinjirin da ya kai ga mutuwarsa.

Za mu maka ta a kotu, yan sanda

Wakil ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda daga bisani za a kai wacce ake zargin kotu don fuskantar hukunci, rahoton The Cable.

Masu Shirin ‘Mata A Yau’ Sun Ziyarci Malam Daurawa Domin Bayar Da Hakuri Ga Al'umma

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira a Jihar Arewa

A wani labari na daban, mun ji cewa a makon da ya gabata ne dai kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka cika da zazzafar muhawara kan wani shiri mai take 'Mata A Yau' da ake gabatarwa a gidan talabijin na Arewa24.

Hakan ya samo asali ne daga bayanin da ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin, Aisha Umar Jajere ta yi dangane da batun gaisuwa tsakanin mata da miji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel