Budurwa Mai Shekara 23 Ta Koka Bayan Ta Kasa Samun Saurayi

Budurwa Mai Shekara 23 Ta Koka Bayan Ta Kasa Samun Saurayi

  • Wata budurwa ta nuna damuwarta bayan ta kai shekarun da yakamata a ce tana soyayya amma samun saurayi ya gagareta
  • Budurwar mai shekara 23 a duniya, ta bayyana cewa tana jin tsoro ko tana da wata matsalar ne, saboda ta kasa samun wanda zai so ta
  • Ta bayyana cewa a halin yanzu kaɗaici ya dameta, amma mutane sun ba ta shawarar ka da ta takura wa kanta

Wata budurwa mai shekara 23 a duniya, ta bayyana cewa har yanzu ta kasa samun soyayya duk da ta daɗe tana nema.

A wani saƙo mai ɓoye suna da ta tura wa wata mai amfani da sunan Chinaza Victoria a Twitter, budurwar ta bayyana cewa yanzu haka kaɗaici ya dameta.

Budurwa ta koka kan rashin saurayi
Budurwar ta shiga damuwa kan rashin saurayi Hoto: Getty Images/Stefanamer. Hoton an yi amfani da shi ne domin misali
Asali: Getty Images

Ta yi tambayar cewa ko har yanzu tana da damar da za ta iya samun soyayya saboda ta kwashe tsawon lokaci tana nema, amma ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

“Dalilin Da Yasa Aka Daina Ganinmu Tare Da Maryam Yahaya”, Amal Ta Fasa Kwai

Duk da cewa da zuciya ɗaya take tunkarar maza, ta bayyana cewa har yanzu ba ta da saurayi, kuma har yanzu ta kasa tsunduma cikin kogin soyayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Budurwa mai shekara 23 ta kasa samun saurayi

Budurwar wacce ta sakaya sunanta, a yanzu ba ta da saurayin da su ke soyayya, wanda hakan yana matuƙar yi mata ciwo.

A kalamanta:

"Wai sai yaushe zan samu soyayya ne? Shekarata 23 kuma ba ni da saurayi. Ina son yin soyayya amma har yanzu ban dace ba. Wai anya komai daidai yake a wajena kuwa?"

Martanin ƴan soshiyal midiya

@ArinzeChukwu_OM ya rubuta:

"Yakamata a na gaya mana daga yankin da mutanen nan su ke da ƙabilunsu. Ba zan bayyana abin da yake raina ba dangane da matsalarta."

@ricuseric ya rubuta:

"Ba ki da matsalar komai.... mutanen da ba su da aikin yi sun mayar da soyayya wani abun tutiya. Ki zama kanki. A shekara 23 yakamata ya yi a ce kin mayar da hankali wajen yin wani muhimmin abu a rayuwarki."

Kara karanta wannan

"Badakalar Miliyan 40": Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

love_Victoria17 ta rubuta:

"Ka da ki takura wa kanki. Za ki samu idan lokacin samun ya yi. Waɗanda ke cikin soyayyar ba ma wani daɗi su ke ji ba. Don haka kada ki damu kanki."

Matashi Ya Fasa Auren Budurwar Da Zai Aura

A wani labarin kuma, wani matashi ya haƙura da auren budurwarsa wacce zai aura bayan ta zo masa da wata gagarumar buƙata.

Matashin dai ya fasa auren ne bayan ta nemi sai ya kashe N17m.wajen shirya shagulgula domin bikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel