Mai POS Ta Sharbi Kuka Da Majina Yayin da Kwastoma Ya Arce Da Wayarta Bayan Ya Tura N500, Bidiyon Ya Yadu

Mai POS Ta Sharbi Kuka Da Majina Yayin da Kwastoma Ya Arce Da Wayarta Bayan Ya Tura N500, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata mai POS ta hadu da bacin rana yayin da ta lura cewa wani kwastoma ya arce da wayarta
  • Matashiyar ta fashe da kuka yayin da take korafin rasa wayarta bayan kwastoman ya yi tranfa din N500
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun tausaya wa mai POS din, yayin da wasu suka bayyana hatsarin da ke tattare da sana'ar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mai POS ta shiga tasku sannan ta zub da hawaye bayan wani kwastoma ya sace mata wayarta.

A cewar matashiyar wacce aka dauka a bidiyo, ta ajiye wayar a kan teburinta yayin da take kula da kwatoman.

Kwastoma ya gudu da wayar mai POS
Mai POS Ta Sharbi Kuka Da Majina Yayin da Kwastoma Ya Arce Da Wayarta Bayan Ya Cire N500, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @precious_eze
Asali: TikTok

Sai dai kuma, bayan ta taimakawa mutumin wajen tura N500, sai ta lura wayarta kirar Android ya yi layar zana.

Yayin da take zubar da hawaye, mai POS din ta koka cewa barawon ya siya cincin da take siyarwa ne. Mutane sun taru a kan matar sannan suka yi kokarin lallashinta.

Kara karanta wannan

Wike Na Hawa Motar Miliyan 300 Wacce Harsashi Bai Ratsa Ta? Ministan Abuja Ya Fayyace Gaskiya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Harma wata mata ta bai wa mai POS din wayarta ta gwada kiran nata layin, amma a kashe yake. Bidiyon ya haifar da martani a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun tausayawa mai POS

@Angel love ta ce:

"Lol wannan ya sa na tuna da lokacin da nake wannan sana'ar. Ina rike wayata da karfi ne."

ChisomRita ta ce:

"Baaba sana'ar POS na da hatsari don Allah, an kashe wata a unguwarmu aka karbe kudinta."

standardkween78 ta ce:

"Wannan abun bakin ciki ne nawa ne albashin da mutum zai dunga rasa wayarsa."

spirax8 ya ce:

"Mutum ta rasa wayarta sannan abun da kika mayar da hankali wajen yi shine daukarta bidiyo yayin da take kuka...mu zama mutane na dan lokaci mana."

Mqnnie Cruz ta ce:

"Na tausaya mata ko da wayar android ce ta yi aiki tukuru ne kafin ta mallaki abun ta."

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Mata Yar Tsurut Tana Tafiya Tare Da Wani Dogon Mutum Ya Bar Mutane Baki Bude

thatboireu ta ce:

"Mai yasa suke mata tambayoyi haka, idan za ku taimaka mata ku taimaka mata ku daina rura wuta a lamarin. Waya wayace imma iphone ko ba shi ba."

Bidiyon wata mata yar tsurut ya dauka hankali

A wani labari na daban, mun ji cewa an gano wata mata yar tsurut tana tafiya a titi tare da wani dogon mutum.

Ajoke Ade ce ta dauki bidiyon matashiyar da mutumin sannan ta yada shi a dandalin TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel