Budurwa 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan An Wawushe Mata N68m a Asusun Ajiyarta Na Banki

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Koka Bayan An Wawushe Mata N68m a Asusun Ajiyarta Na Banki

  • Wata budurwa ƴar Najeriya wacce ta rayu a ƙasar Italy tsawon shekara 13 ta bayyana wani abun takaici da ya faru da ita a bankin Najeriya
  • Budurwar mai suna, Glory Omokaro, ta tafi ƙasar Italy a shekarar 2005 sannan ta kawo ziyara a Najeriya a shekarar 2013 domin buɗe asusu a banki
  • Glory ta yi iƙirarin cewa ta ajiye N68m a asusun, amma lokacin da ta dawo Najeriya a watan Mayun 2023, sai ta tarar da N3,000 kacal

Wata budurwa wacce take rayuwa a ƙasar Italy, ta ajiye N68m a asusun ajiyar bankinta na Najeriya, amma ta rasa kuɗin gaba ɗaya.

A wani bidiyo da a ka sanya a TikTok, an bayyana cewa budurwar mai suna Glory Omokaro, ta tafi ƙasar Italy a shekarar 2005. Ta yi aiki tuƙuru wajen samun kuɗi, inda ta riƙa ajiyesu a asusun ajiyarta na wani banki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Budurwa ta koka bayan an wawushe mata kudi a banki
Sama da N68m a ka wawushe na budurwar a banki. Hoto: Getty Images/Jasmin Merdan and Bloomberg. Hoton an yi amfani da shi ne kawai domin misali
Asali: Getty Images

Glory ta buɗe asusun ajiyar ne lokacin da ta kawo ziyara a Najeriya a shekarar 2013, inda ta fara adana kuɗinta a ciki. Ta buɗe asusun ajiyar ne a birnin Benin na jihar Edo, bayan ta ziyarci ƴan uwanta.

Glory ta ajiye kuɗi a asusun har sai da suka kai N68m, inda ta yi fatan ta yi amfani da su bayan ta dawo Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan ta dawo Najeriya a watan Mayun 2023, sai ta tarar da cewa N3000 kawai suka rage a cikin asusun ajiyar na ta.

Yadda aka wawushe N68m a asusun Glory

A shekarar 2021, katin ATM ɗinta ya lalace, inda ta kira manajan bankin ya taimaka mata ta sabunta shi, amma ya gaya mata cewa dole sai ta zo da kanta.

A dalilin annobar korona da a ke fama da ita a lokacin, Glory ba ta samu zuwa Najeriya ba a lokacin.Lokacin da ta dawo Najeriya a watan Mayun 2023, N3000 ne kawai suka rage a asusun.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Abubuwan Sani Dangane Da Minista Mafi Karancin Shekaru a Cikin Ministocin Tinubu

Ta buƙaci a ba ta bayanin asusun, inda ta gano cewa an riƙa fitar da ƙudin ne daga cikin asusun. Ɗan uwan Glory shi ne ya bayyana labarin a Brekete Family Radio.

Budurwa Ta Samu N25k

A wani labarin kuma, wata budurwa ta cika da murna bayan ta samu maƙudan kuɗaɗe a yanar gizo.

Budurwar dai ta samu N245k a Twitter a wani sabon tsarin raba kuɗin da a ka samu ta hanyar talla a manhajar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel