Shugaba Bola Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Ministocinsa

Shugaba Bola Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Ministocinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da sabon gargaɗi ga Nyesom Wike da sauran ministoci 44 da ya rantsar a ranar Litinin
  • Ƙasa da sa'o'i 48 bayan ya rantsar da majalisar ministocinsa, Shugaba Tinubu ya tunatar da ministocin shi ne direban jirgi ko motar da su ke ciki
  • Wike, jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya yi maganganu kan muƙamin da ya samu da abin da ƴan Najeriya za su yi tsammanin samu daga wajensa a matsayin ministan Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Aso Rock, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da gargaɗi mai ƙarfi kan sabbin ministoci 45, ciki har da Nyesom Wike, ministan birnin tarayya Abuja.

Gargaɗin na shugaban ƙasar na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 48 bayan ya rantsar da majalisar ministocinsa a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Uwargidan Tinubu Ta Yi Magana Kan Halin Ƙuncin Da Ake Ciki a Najeriya, Ta Fadi Abinda Zai Faru a Gaba

Shugaba Tinubu ya gargadi ministocinsa
Shugaba Tinubu ya bukaci ministocinsa su jajirce Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

A cikin wata wallafa a Twitter ranar Talata, 22 ga watan Agusta, Shugaba Tinubu ya gayawa ministocin cewa ƴan Najeriya sun ƙosa su ga an cika alƙawuran da aka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.

Tinubu ya bayyana cewa da shi da ministocin duk suna cikin jirgi ɗaya ne ko mota dangane da sabon aikin da ke gabansu, amma ya tunatar da su cewa shi ne direba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Tinubu ya tunatar da sabbin ministoci 45

A yayin da ya sanya bidiyon da aka ɗauka wajen rantsar da ministocin, shugaban ƙasar ya tunatar da su cewa dole ne su zama alƙalan kansu kafin ƴan Najeriya su yi musu alƙalanci sannan ya yi musu addu'ar samun nasara.

Shugaban ƙasar ya rubuta cewa:

"A cikin wannan sabon aikin, muna cikin wannan jirgin a tare, ko da kuwa mota ce, ni ne direban. Gaba ɗaya ƙasa an zura mu ku ido. Dole ne mu haɗu wajen sauke nauyin da ke kan mu. Yana da kyau mu yi aikin nan domin cika fatan da ƴan Najeriya ke da shi. Allah ya yi jagora, Allah ya albarkaci tarayyar Najeriya."

Kara karanta wannan

Sabon Ministan Shugaba Tinubu Ya Ce Zai Yi Aiki Kamar Magini a Yayin Da Ya Shiga Ofis

Bwala Ya Gargadi Wike

A wani labarin kuma, hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gargaɗi Nyesom Wike, sabon ministan birnin tarayya Abuja.

Daniel Bwala ya gargaɗi Wike cewa ya bi a hankali domin Abuja ba Fatakwal ba ce, inda zai ci karensa babu babbaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel