Ministocin Tinubu: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministoci Su Yi Murabus Ida Ba Za Su Iya Ba

Ministocin Tinubu: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministoci Su Yi Murabus Ida Ba Za Su Iya Ba

  • Wata ƙungiya mai suna The Natives ta yi muhimmin kira ga sabbin ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa
  • Ƙungiyar ta ja kunnen ministocin cewa su yi murabus da zarar sun kasa sauke nauyin da aka ɗora musu
  • Ƙungiyar ta yi musu fatan samun nasara wajen sauke wannan nauyin da ya hau kansu na ciyar da ƙasar nan gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An buƙaci ministocin Shugaba Tinubu da su yi murabus idan har sun san ba za su iya taimakawa ba wajen cimma ajandar gwamnatin nan ba ta "Renewed Hope".

Ƙungiyar wasu masu kishin dimokuraɗiyya mai suna The Natives, ita ce ta yi wannna kiran a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja, yayin ganawa da manema labarai.

An bukaci ministocin Tinubu su yi murabus
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Da yake magana a wajen, shugaban ƙungiyar, Hon, Smart Edwards, ya buƙaci ministocin da su yi koyi da irin halin shugabanci nagari na Shugaba Tinubu, ko su rasa muƙamansu.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Hango Wani Sabon Abu Da Zai Faru a Mulkin Shugaba Tinubu

"Wannan karon dole ƴan Najeriya su yi nasara", cewar ƙungiyar

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun yi amanna da ajandar 'Renewed Hope' ta wannan gwamnatin, saboda haka za mu bayar da dukkanin goyon baya, za mu riƙa bibiya da sanya ido kan ayyukanku, ba za mu ji tsoron yi muku gyara ba ko kiran a kore ku. A wannan karon, dole ƴan Najeriya su yi nasara."
"Gaba ɗaya ƙasar nan tana da tarin fata a kan ku, haka shugaban ƙasa, muna fatan ku yi mulki mai nasara."
"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shi ƙoƙarin, yana da alhakin sanya ido da duba yadda lamura ke gudana, sannan duk wata nasara ko akasinta da aka samu, hakan yana a wuyansa ne."

Edward ya ƙara da cewa dole ne ƴan Najeriya su san an samu sauyi, inda ya ƙara da cewa sun daɗe suna zaman jiran tsammani saboda hak sun cancanci su wala ba sake shiga cikin halin shan wuya ba.

Kara karanta wannan

Uwargidan Tinubu Ta Yi Magana Kan Halin Ƙuncin Da Ake Ciki a Najeriya, Ta Fadi Abinda Zai Faru a Gaba

Ministocin Tinubu Za Su Lakume Kusan N9bn

A wani labarin kuma, an bayyana adadin yawan kuɗin da za a kashewa ministocin Shugaba Tinubu kafin su bar.ofis.

Ministocin dai za su laƙume maƙudan kuɗi har N8.63bn na albashi da alawus a cikin shekara huɗu da za su yi a kan muƙamamsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng