Manyan Labarai A Yau
Jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa gwangwaje yankin Kudu maso Gabas da muƙaman manyan ministoci a gwamnatinsa.
Ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi (NULGE) ta shiga yajin aikin sai baba ta gani a jihar Plateau bisa abin da ta kira tsoron rikicin da ka iya aukuwa a jihar.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da aka shigar kan gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, na neman a soke nasararsa.
Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Taraba, Cif Victor Bala Kona, ya yi bankwana da duniya bayan fama da jinyar rashin lafiya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana adadin gangar man fetur da miyagun ɓata-gari su ke sacewa kullum a ƙasar nan.
Wata matashiyar budurwa ta fito da gaba daya kayanta da ke nuna tsaraici sannan ta cinna masu wuta. Ta ce a yanzu ta shiryu ta zama cikakkiyar Kirista ta gaske.
Matsala babba ta tunkaro ministar al'adu da fasaha ta shugaɓa Tinubu bayan hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NƳSC) ta tabbatar cewa ba ta kammala bautar ƙasa ba.
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP, ya yi zargin cewa bayanan jami’ar jihar Chicago na shugaba Tinubu ya yi karo da abun da ya gabatar a 1999.
Wasu miyagun ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sjn sace mutum biyu a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Ƙaduna.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari