Kasar Faransa Ta Haramta Dalibai Sanya Hijabi a Makarantun Gwamnati

Kasar Faransa Ta Haramta Dalibai Sanya Hijabi a Makarantun Gwamnati

  • Kasar Faransa ta shirya haramta ɗalibai mata musulmai sanya hijabi a makarantun gwamnati na ƙasar
  • Ministan ilmin ƙasar Gabriel Attal, shi ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Agustan 2023 a yayin wata tattaunawa
  • Ministan ya bayyana cewa zai yi magana da makarantu a cikin satin da zai kama domin ganin yadda za a tabbatar da haramcin sanya hijabin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kasar Faransa - Gwamnatin ƙasar Faransa ta haramta ɗalibai sanya ɗalibai musulmai sanya hijabi a makarantun gwmanatin na ƙasar.

Gabriel Attal, ministan ilmi na ƙasar Faransa ya bayyana hijabi a matsayin wata alamar addini ce wacce take kawo barazana ga tsarin kafa makarantu kan yi wa kowane addini adalci.

Faransa ta haramta sanya hijabi
Kasar Faransa ta hana dalibai sanya hijabi a makarantun gwamnati Hoto: @EmmanuelMacron
Asali: Twitter

Hijabi na kawo wariya, cewar Attal

"Idan ka shiga cikin aji, bai kamata ka iya gane addinin da ɗalibai su ke bi ba ta hanyar kallonsu." A cewar Attal.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Abun Alkairin da Zai Faru Kan Man Fetur a Karshen 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na yanke hukuncin cewa an dai na sanya hijabi a makarantu."

TRTWorld ta rahoto cewa ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talbijin ta TF1 TV a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa zai bayar da cikakkun bayanai kan yadda makarantun za su tabbatar da haramcin sanya hijabin.

Ƙasar Faransa tana da tsauraron matakai kan alamomin da su ke nuna bambancin addini a makarantun gwamnati da wuraren aiki na gwamnati, bisa cewa sun saɓa dokokin yi wa addinan ƙasar adalci.

Tuni gwamnatin ƙasar ta cire koyar da al'adun ɗariƙar Katolika a makarantu, yayin da aka haramta sanya adiko a shekarar 2004.

A shekarar 2010, gwamnatin ƙasar ta haramta sanya niqabi, wanda hakan ya sanya musulman ƙasar suka yi ta sukar matakin gwamnatin.

Wannan sabuwar dokar akan hijabi a na sa ran za ta fata aiki ne a ranar 4 ga watan Satumba, lokacin da sabuwar shekarar karatu za ta fara a ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

El-Zakzaky Ya Zargi Faransa Da Amurka

A wani labarin na daban kuma, jagoran mabiya shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya zargi ƙasashen Faransa da Amurka da hura wutar rikicin Jamhuriyar Nijar.

El-Zakzaky ya bayyana cewa ƙasashen biyu ba irin munafurcin da ba su sani ba wurin haddasa yaƙi idan damar hakan ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel