Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Jihar Taraba Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Jihar Taraba Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Taraba ta shiga cikin jimamin babban rashin da ta yi
  • Hakan na faruwa ne bisa rasuwar da tsohon shugaban jam'iyyar na jihar, Cif Victor Bala Kona, ya yi a Abuja
  • Shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Inuwa Bakari, ya tabbatar da mutuwarsa, inda ya yi nuni da cewa marigayin ya mutu ne bayan fama da rashin lafiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jalingo, jihar Taraba - Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Taraba, Cif Victor Bala Kona, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar New Telegraph ta rahoto cewa jigon na jam'iyyar PDP, ya mutu ne a safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Agustan 2023, a birnin tarayya Abuja.

Tsohon shugaban PDP ya mutu
Marigayi Victor Bala Kona ya mutu bayan jinya a Abuja Hoto: Tony Matinjah, Office of The SA Media and Digital Communications, Taraba State
Asali: Facebook

Da yake magana kan wannan babban rashin, muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Taraba, Alhaji Inuwa Bakari, ya tabbatar da mutuwar Bala Kona, inda ya ƙara da cewa ya bar duniya ne bayan ya yi fama da jinya.

Kara karanta wannan

An Shiga Jimami Bayan Dan Shugaban Jam'iyyar APC Ya Rasu Tare Da Abokinsa a Wani Mummunan Hatsarin Mota

"Abun takaici ne", cewar shugaban PDP na Taraba

An rahoto cewa a baya an fitar da tsohon shugaban jam'iyyar zuwa ƙasar waje domin duba lafiyarsa, sai dai cikin ƴan kwanakin nan an dawo da shi gida Najeriya inda a nan kwanansa suka ƙare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga jam'iyyar, Bakari ya yi nuni da cewa jam'iyyar za ta yi kewarsa sosai, cewar rahoton Channels tv.

"Abun takaici ne ya tafi ya bar mu a daidai lokacin da mu ke buƙatar ƙwarewarsa wajen shugabanci da siyasa." Cewar Bakari.

Shi ma da yake nasa martanin, Emmanuel Bello, mai ba gwamnan shawara na musamman kan kafafen sadarwa, ya yi ta'aziyyar rasuwar mamacin a shafinsa na Facebook.

A kalamansa:

"Labarin baƙin cikin mutuwar tsohon shugaban jam'iyyar mu, Cif Victor Bala Kona, yana da matuƙar ciwo."

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Kunno a Jam'iyyar NNPP, Shugabannin Jam'iyyar Sun Ja Kunnen Kwankwaso Kan Abu 1

Dan Shugaban APC Ya Rasu

A wani labarin kuma, ɗan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Sokoto, ya riga mu gidan gaskiya.

Anas Isa Sadiq Acida ya rasu ne tare da abokinsa a wani mummunan hatsarin mota. Matasan guda biyu suna kan hanyarsu ta dawowa gida ne daga birnin Ibadan inda su ke yin karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng