Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Mutum Biyu a Zariya

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Mutum Biyu a Zariya

  • Masu garkuwa da mutane sun sake kai farmaki a gundumar Wusasa cikin ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduma
  • Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da wani ma'aikacin wani asibiti tare da ƙaninsa a yayin harin
  • Gundumar Wusasa ta daɗe tana fama da matsalar hare-hare ƴan bindiga inda take zama hanyar da miyagu ke kai hari a wasu unguwannin Zariya

Zariya, jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kai farmaki a gundumar Wusasa da ke ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Masu garkuwa da mutanen a yayin harin da suka kai, sun sace wani ma'aikacin wani asibiti mai suna St. Luke, mai suna Yusha'u tare da ƙaninsa mai suna Joshua Peter.

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane a Zariya
Masu garkuwa da mutanen sun kai harin ne cikin dare Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa sarkin Wusasa, Injiniya Isiyaku Ibrahim, ya tabbatar da aukuwar harin da maharan suka kai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Arewa

Sarkin ya bayyana cewa maharan sun dira a unguwar ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare, sannan suka riƙa harbe-harbe kafin su wuce su tasa ƙeyar mutum biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƴan bindiga na yawan wucewa ta Wusasa

Unguwar Wusasa wasu da yawa na ganin cewa ita ce hanyar da mahara ke amfani suna kai hare-hare a mafiya lokutan da su ke kai hare-hare a unguwannin birnin Zariya.

Mutum biyun da masu garkuwa da mutanen suka ɗauke dai, asalinsu ƴan ƙaramar hukumar Ikara ne ta jihar Kaduna, sannan an taɓa sace mahaifinsu a gidansu da ke garin.

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda jihar Kaduna ba, Mohammed Jalige, saboda rashin samun wayarsa da aka yi.

Matsalar rashin tsaro ba baƙuwa ba ce a gundumar Wusasa, inda ƴan bindiga ke yawan kai hare-hare, kashe bayin Alƙah da ɗauke mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Yan Bindiga Sun Sace Jigon APC

A wani labarin kuma, wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da sakataren tsare-tsare na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ihar Ƙaduna.

Ƴan bindigan sun dai bi Ibrahim Kawu Yakasai ne har cikin gidansa sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel