Hannatu Musawa: Babban Lauya Ya Yi Magana Kan Dambarwar Da Ministar Take Ciki

Hannatu Musawa: Babban Lauya Ya Yi Magana Kan Dambarwar Da Ministar Take Ciki

  • Hannatu Musawa, ministan fasaha, al'adu ba ta buƙatar satifiket fin NYSC kafin a naɗa ta muƙamin siyasa, a cewar Barr. Festus Ogun
  • Ƙungiyar kare haƙƙin marubuta ta Najeriya (HURIWA) ta yi zargin cewa ministar ƴar bautar ƙasa ce wacce ba ta kammala ba
  • Sai dai, Barr. Ogun ya bayyana cewa a hukuncin kotun ƙoli, muƙamin siyasa ba daidai yake da aikin gwamnati ba

FCT, Abuja - Wani lauyan kundin tsarin mulki, Festus Ogun, ya bayyana cewa mutane ba su buƙatar satifiket ɗin kammala bautar ƙasa (NYSC), kafin a ba su muƙamin siyasa.

Ogun yana martani ne a kan dambarwar da ake yi kan matsayin kammala bautar ƙasa na ministan fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa.

Lauya ya yi magana kan dambarwar Hannatu Musa Musawa
Hannatu Musa Musawa tare da Shugaba Tinubu Hoto: @HanneyMusawa
Asali: Twitter

Musawa ba ta bukatar NYSC domin zama minista

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu Ka Iya Rasa Mukaminta Yayin Da NYSC Ta Bayyana Matakin Dauka Na Gaba Bayan Ta Tabbata Yanzu Take Bautar Kasa

Wannan dambarwar dai ta ƙara yin yawa ne bayan hukumar ƴan yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa ministan yanzu take yin bautar ƙasarta, wanda hakan ya sanya aka yi ta caccakarta da neman ta ajiye muƙaminta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Eddy Megwa, darektan hulɗa da jama'a na hukumar, ya yi magana kan dambarwar inda ya bayyana cewa riƙe muƙamin ministan da Musawa take yi ya saɓawa dokar hukumar.

Megwa ya yi bayanin cewa saɓa dokar hukumar ne masu yi wa ƙasa hidima su karɓi kowane irin muƙamin gwamnati a yayin da su ke yi wa ƙasa hidima.

Amma Ogun ya bayyana cewa satifiket ɗin NYSC ana buƙatar shi ne kawai domin samun aiki a ma'aikatun gwamnati da na masu zaman kansu.

Ya rubuta a shafinsa na X (wanda a baya a ka sani da Twitter), a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta cewa:

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Wani Yanki Ya Huro Wuta Sai Ya Samu Kujerar Minista, Ya Bayyana Kwararan Dalilai

"Ba ka buƙatar satifiket ɗin NYSC domin samun muƙamin siyasa. Ana buƙatar sa ne kawai domin samun aiki a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu. A cewar kotun ƙoli muƙamin siyasa ba daidai yake da samun aiki ba."

Hannatu Musawa Ta Magantu

A wani labarin kuma, Hannatu Musa Musawa ta fito fili ta ƙaryata raɗe-raɗin cewa ta yi martani kan cece-kucen da ake yi dangane da zamanta minista tana ƴar bautar ƙasa.

Ministar ta bayyana cewa labarin da ke yawo cewa ta yi martani dangane da batun da ake ta cece-kuce a kanta, ba daga gareta ya fito ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel