Manyan Labarai A Yau
Minista babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya magantu kan shirinsa na gaba idan kotu ta ƙwace nasarar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023.
Bidiyon wani jami’in dan sanda a jihar Adamawa yana sharbar kuka karamin yaro bayan an sallame shi daga aiki saboda aikata ba daidai ba ya haddasa cece-kuce.
Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta gargadi sojojin Najeriya kan koyi da sojojin kasar Gabon da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba.
Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN) ya ce matsin talauci ne abinda ya janwo ake ta samun juyin mulki a kasashen Afirka.
Gwamnatin jihar Delta ta fito fili ta yi magana kan rahotannin da ke yawa cewa kotu ta ƙwace nasarar da gwamna Sheriff Oborevwori ya samu a zaɓen gwamnan jihar.
Shugaban cocin Glorious Mount of Possibility Church, Fasto David Elijah, ya ja kunnen ɗan takarar shugaban ƙasa, na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
Juyin mulki ya dawo a Nahiyar Afirika inda sojoji ke cigaba da hamɓarar da gwamnatin fararen hula. Tun daga shekarar 2020 sojoji sun hamɓarar da gwamnatoci 9.
Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya bayyana hanyar da ECOWAS da AU za su bi don hana sojoji karbe mulki a Afrika. Ya yi martani kan Gabon.
Nyesom Wike, ministan Abuja ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurce shi da ya farfado da FCT. A ranar 16 ga watan Agusta ne aka nada Wike ministan Abuja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari