"Na Ji Dadin Juyin Mulkin Gabon", Fayose Ya Yi Martani Mai Zafi

"Na Ji Dadin Juyin Mulkin Gabon", Fayose Ya Yi Martani Mai Zafi

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi martani a kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Gabon
  • Fayose ya bayyana a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, cewa ya yi matukar farin ciki da hambarar da gwamnatin Ali Bongo da sojoji suka yi
  • Sai dai kuma, dan siyasar ya ce baya goyon bayan sojoji su rika tsoma baki a harkar siyasa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya nuna jin dadinsa dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Gabon da ke Afrika ta tsakiya.

Fayose ya yi martani a kan hambarar da gwamnatin farar hula da sojojin suka yi a kasar Gabon a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, rahoton Punch.

Fayose ya nuna farin cikinsa a kan juyin mulkin Gabon
"Na Ji Dadin Juyin Mulkin Gabon" - Fayose Ya Yi Martani Mai Zafi Hoto: Ayodele Fayose, The Instigator @Am_Blujay
Asali: Facebook

A ranar Laraba ne wasu manyan sojoji suka bayyana a talbijin din kasar Gabon inda suka sanar da soke sakamakon zaben da Ondimba Ali Bongo ya yi nasara sannan suka kuma soke duk gaba daya hukumomin kaar.

Kara karanta wannan

"Mu Makota Ne" Shugaba Tinubu Ya Bude Gaskiya Kan Yaki da Sojojin Jamhuriyar Nijar

Sanarwar na zuwa ne bayan Shugaba Ali Bongo mai shekaru 64 ya sake lashe zabe a karo na uku, wanda ya kara wa'adin shekarun da iyalinsa suka kwashe suna shugabantar kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar adawar kasar ta zargi jam'iyya mai mulki da tafka magudi a zaben da ya gabata.

Iyalan Bango, daya daga cikin daula mafi iko a Afrika ne a kan karagar mulkin kasar tun daga 1967.

Bana goyon bayan sojoji su tsoma baki a harkar siyasa

Da yake jawabi a gidan talbijin na Channels, Fayose ya ce baya goyon bayan sojoji su tsoma baki a harkar siyasa, yana mai cewa yawaitar juyin mulkin da aka yi a Afirka a baya-bayan nan alama ce ta rashin zaman lafiya.

Fayose ya ce:

"Ina matukar farin ciki da abun da ya faru a Gabon. Bana son sojoji suna tsoma baki a siyasa amma ina so na fada maku cewa Najeriya daban ce, muna da ingantacciyar dimokradiyya.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

“Muna da kurakuran mu amma kuna iya ganin tsarin dimokradiyya da babu tangarda. Bayan shekaru hudu za a yi zabe… Najeriya ta fita daga wannan jam’iyya zuwa wata jam’iyya.
"Daga wannan mutumin zuwa wani mutum a cikin yan tsakakkani. Amma a wata kasa inda mutum daya ya shafe shekaru 30, 40. Ya zama dole a yi waje da shi ta kowace hanya.
“Wannan ya bambanta da yanayin Najeriya. Najeriya ta mika wuya amma har yanzu ba mu kai ga karshe ba.”

Tinubu ya magantu kan juyin mulkin da sojoji ke yi a Afrika

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa tsoron da ya dunga ji game da juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar ya tabbata da abun da ya faru a Gabon inda sojoji suka tsige Shugaba Ali Bongo ta hanyar kifar da gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya ce ya yi fargabar cewa matakin da sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar suka dauka zai kafa mummunan tarihi ga nahiyar bakar fata. Fadar shugaban kasa ta bayyana haka a cikin wata wallafa a manhajar X.

Asali: Legit.ng

Online view pixel