Da Gaske Ministan Birnin Tarayya Wike Ya Bada Umarnin Rushe Tashar Motar Jabi Da Ke Abuja?

Da Gaske Ministan Birnin Tarayya Wike Ya Bada Umarnin Rushe Tashar Motar Jabi Da Ke Abuja?

  • Wani bidiyon TikTok da ke yawo ya yi ikirarin cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi umurnin rusa tashar motar Jabi da ke Abuja
  • Sai dai kuma, wani bincike ya nuna cewa bidiyon tun daga 2020 ne lokacin da hukumar babbar birnin tarayya ta yi umurnin rushe shagunan da basa bisa ka'ida a tashar
  • Bincike ya kuma gano cewa babu wani aikin rusau da ke gudana a wannan sashi na tashar da ake ta yayatawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wani bidiyo da ke yawo yanzu haka a TikTok ya yi ikirarin cewa sabon ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi umurnin rusa tashar motar Jabi da ke Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wani da ke magana a cikin bidiyon ya koka cewa "an rushe shaguna" kuma "an kona kasuwanci" biyo bayan umurnin da ake zargin gwamnati ta bayar.

Kara karanta wannan

“Karya Ne Ban Ba Da Umurnin Sakin Matan Yan Bindiga Ba”, Gwamnan Arewa Ya Magantu

Bincike ya nuna a yanzu haka ba a aikin rusa tashar mota na Jabi
Da Gaske Ministan Birnin Tarayya Wike Ya Bada Umarnin Rushe Tashar Motar Jabi da ke Abuja? Hoto: @GovWike, @Abuja_Facts
Asali: Twitter
"Shin gwamnatin na so mu zama bata gari ne a cikin al'umma? Mun samu sana'a don rike kanmu amma gwamnati ta zo za ta kunyata shi. Ba za mu zama bata gari ba za mu ci gaba da aiki amma ya kamata gwamnati ta duba wannan lamari," cewar mutumin.

Shin da gaske Wike ya yi umurnin rushe tashar motar Jabi?

Daily Trust ta bayyana cewa wani binciken da ta yi na zamani ya nuna cewa an fara fitar da bidiyon ne a 2020 lokacin da hukumar birnin tarayya ta yi umurnin rusa shaguna da basa bisa ka'ida a tashar motar Jabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta kuma bayyana cewa a 2022 an rushe Jabi Art Village da gine-ginen da basa bisa ka'ida a Jabi Dakibiyu.

Hakazalika, jaridar ta kara da cewar bincikenta ya nuna cewa babu wani aikin rusau da ke gudana a sashin tashar da ake rade-radin ana rusawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi, Ta Bayyana Dalilanta

Ta rufe da cewar bidiyon da ke yawo wanda ke cewa Wike ya fara aikin rusau a tsahar motar Jabi karya ne da batarwa.

Shehu Sani ya shawarci Wike kan rushe-rushe

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon dan majalisar tarayya Shehu Sani, ya ja kunnen tsohon ministan Abuja Nyesom Wike.

Ya ce Wike mutum ne jajirtacce a duk aikin da ya sanya a gaba, sai dai ya yi gargadin cewa zai iya janyowa kansa da Tinubu matsaloli masu girma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel