Dan Najeriya Ya Makale a Birtaniya Bayan Matarsa Da Ke Cin Amanarsa Ta Soke Bizarsa Don Auren Wani Daban

Dan Najeriya Ya Makale a Birtaniya Bayan Matarsa Da Ke Cin Amanarsa Ta Soke Bizarsa Don Auren Wani Daban

  • Wani magidanci na fuskantar yiwuwar korarsa daga Birtaniya bayan matarsa ta soke bizarsa
  • Rigima ya fara ne bayan mutumin ya gano matarsa tana cin amanarsa, lamarin da yasa ta gaggauta neman a raba aurensu don kasancewa tare da saurayin nata
  • An yada kwafin wasikar da ofishin kula da harkokin gida na Birtaniya ya gabatarwa mutumin a soshiyal midiya yayin da mutane suka yi martani kan lamarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya ya shiga damuwa bayan matarsa da ke cin amanarsa ta soke bizarsa na Birtaniya.

Wani mai amfani da shafin Twitter, @Wizarab10, wanda ya yada labarin, ya bayyana cewa mutumin ya gano cewa matarsa na cin amanarsa.

Matashi na gab da hakura da zaman UK bayan matarsa ta soke bizarsa
Dan Najeriya Ya Makale a Birtaniya Bayan Matarsa Da Ke Cin Amanarsa Ta Soke Bizarsa Don Auren Wani Daban Hoto: FJ Jimenez, Twitter/@Wizarab10
Asali: Getty Images

Sai kuma matar tasa da ke cin amanara ta shigar da karar neman a raba aurensu a kokarinta na kasancewa tare da saurayin nata sannan ta sanar da ofishin kula da harkokin cikin gida na Birtaniya.

Kara karanta wannan

"Shi Ya Dauki Nauyin Karatuna": Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu

A wata wasika da aka gabatar a soshiyal midiya, ofishin kula da harkokin gidan ya sanar da mutumin batun soke bizarsa da kuma ba shi tsakanin yanzu zuwa 23 ga watan Oktoba ya nemi sabon biza idan yana son ci gaba da zama a Birtaniya ko kuma ya bar kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lamarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani kan labarin ma'auratan Birtaniya

@Toobbss ya ce:

"Abun dariya, mata za su ci gaba da cewar ba dukka mata ne za su yi wannan ba.
"Ana nan ana nan yan makonni baya, lamari makamancin wannann zai sake faruwa."

@Funmiscute ta ce:

"Baaba ji abun da karfin iko zai iya yi. Wannan mugunta ce daga bangarenta. Ina fatan mutumin zai samu wani abun da zai rike shi. Bai cancanci wannan muguntar ba. Bana ganin laifin duk wani namiji da ya guji mace kirki sabod dalilai irin wannan."

Kara karanta wannan

“Na Gaji Da Su”: Wani Dan Shekaru 55 Ya Saki Matansa 3 a Rana Daya, Ya Fallasa Zunubansu a Bidiyo

@omalichanna ta ce:

"Zan ba shi shawarar ya nemi wani aikin, ya shigar da kara kotu, ya tuntubi lauyan shige da fice cikin gaggawa. Akwai hanyar da za a taimaka masa da shi.''

@KinqKudos ya ce:

"Shin karshen hanyarsa kenan ko akwai abun da zai iya yi da zai taimaka masa da samun sabon biza?"

Ma'aurata 7 sun hada shagalin bikinsu saboda tsadar rayuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa masu bauta a cocin All Saints Kyamwee Anglican da ke gudunmar Machakos sun halarci wani biki na musamman da ya hada ma'aurata bakwai.

A cewar NTV, ma'auratan sun ce sun yarda su yi biki na hadin gwiwa domin ragewa juna zafi saboda tsadar rayuwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel