Gwamna Uba Sani Ya Umarci Yan Sanda Su Binciko Wadanda Sukai Kai Hari a Masallaci

Gwamna Uba Sani Ya Umarci Yan Sanda Su Binciko Wadanda Sukai Kai Hari a Masallaci

  • Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa masallata a ƙaramar hukumar Ikara ta jihar
  • Gwamnan ya ba jami'an ƴan sanda umarnin yin bincike kan harin wanda ya salwantar da rayukan mutum bakwai
  • Malam Uba Sani ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta magance matsalar tsaro a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, a ranar Lahadi ya bayar da umarni ga ƴan sanda da su yi bincike kan harin da aka kai a ƙauyen Saya-Saya na ƙaramar hukumar Ikara ta jihar.

Harin na ƙauyen Saya-Saya dai ya yi sanadiyyar halaka mutum bakwai ciki har da masu gudanar ibada a masallaci.

Gwamna Uba Sani ya ba yan sanda sabon umarni
Gwamna Uba Sani ya umarci yan sanda su yi bincike kan harin na kauyen Saya-Saya Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan, Mohammed Lawal Shehu, ya fitar a Kaduna ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Muje Zuwa: Shehu Sani Ya Bayyana Jam'iyyar Da Za Ta Ci Ribar Rikicin Siyasar Da Ke Tsakanin Gwamnan PDP Da Mataimakinsa

Uba Sani ya yi Allah wadai da harin

Gwamnan wanda ya bayyana kisan a matsayin mugunta da rashin imani, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai zaman lafiya ya dawo a dukkanin sassan jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Mun fahimci damuwa da tashin hankalin da mutane su ke ciki, musamman na Ikara da jihar Kaduna baki ɗaya. Kare lafiyarku da dukiyoyinku shi ne abu mafi muhimmanci a gare mu. Muna ƙara ba ku tabbacin cewa muna aiki tuƙuru domin ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo a jihar nan."
"Muna kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu sannan su sanya ido sosai a wannan lokacin. Muna kira ga jama'a da su ba jami'an tsaro haɗin kai, da bayar da bayani mai muhimmanci wanda zai taimaka wajen binciken da ake yi."

Kara karanta wannan

“Karya Ne Ban Ba Da Umurnin Sakin Matan Yan Bindiga Ba”, Gwamnan Arewa Ya Magantu

A ranar Juma'a da daddare ne dai ƴan bindiga suka kai farmaki ƙauyen lokacin da ake yin Sallar Isha'i a wani masallacin ƙauyen.

Ƴan bindigan sun halaka shugaban ƴan sakai na ƙauyen, limamin da ke jagorantar Sallar da wasu masallata mutum uku, kafin su ƙara halaka wasu mutum biyu a cikin ƙauyen.

Gwamnan Katsina Ya Raba N20m Ga Iyalan Yan Sakai

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Katsina ya raba N20m ya iyalan ƴan sakai da suka rasa ransu wajen samar da tsaro a jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayar da tallafin kuɗin ne ga iyalan ƴan sakai 33 da suka rasu a bakin aiki a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel