Budurwa Yar Shekaru 25 Ta Siya Gida, Ita Ta Fara Mallakar Gida a Danginsu, Bidiyon Ya Tsuma Zukata

Budurwa Yar Shekaru 25 Ta Siya Gida, Ita Ta Fara Mallakar Gida a Danginsu, Bidiyon Ya Tsuma Zukata

  • Bidiyon gwagwarmayar da wata matashiyar budurwa yar shekaru 25 ta sha wajen siyan gidanta na farko ya sace zukatan mutane da dama a TikTok
  • Buduwar ta yada wani bidiyonta tana sanya hannu kan takardar gidan da take mafarkin mallaka, tana mai bayyana yadda ta yi aiki tukuru don cimma haka
  • Ta kuma zaga da masu kallo don nuna masu cikin sabon gidan nata, wanda ya sha kayan alatu

Wani bidiyo mai tsuma zuciya na wata matashiya da cimma mafarkinta na mallakar gidanta na farko ya yadu a TikTok, inda dubban mutane suka kalla da yin sharhi.

An hasko matar mai shekaru 25, wacce ta yi aiki tukuru don tara kudin siyan gidan, tana sanya hannu kan takardun sabon gidanta, tana mai nuna farin ciki da godiyanta.

Kara karanta wannan

"Shi Ya Dauki Nauyin Karatuna": Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa ta mallaki gidan da take mafarkin samu a rayuwa
Budurwa Yar Shekaru 25 Ta Siya Gida, Ita Ta Fara Mallakar Gida a Danginsu, Bidiyon Ya Tsuma Zukata Hoto: TikTok/@lifesqhenry
Asali: TikTok

Ta kuma nunawa mabiyanta cikin hadadden gidan nata, wanda ke da falo, kicin na zamani da hadadden dakin bacci.

Budurwa ta zama ta farko da ta siya gida a danginta

An yi wa bangon gidan fenti da kaloli masu kyau kuma cikin gidan ya sha alatu da kayatarwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon shaida ne ga jajircewa da sadaukarwar matar inda ta zaburar da mutane da dama don cimma burinsu.

Legit.ng ba za ta iya tabbatar da wannan ikirari ba kai tsaye a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli hadadden bidiyon gidan a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da budurwa ta mallaki gidanta na farko

Michelle Watson ta yi martani:

"Wannan irin hadadden gida na taya ki murna sarauniya."

Jay_ lyrical777 ta rubuta:

"Na so wannan na taya ki murna kyakkyawa kin cancance shi."

Kara karanta wannan

Yadda Likitoci Suka Gano Tana Mai Rai A Kwakwalwar Wata Mata

Jamie.V ta yi martani:

"Na taya ki murna yan mata karin nasara amin."

User6346858671812 ta yi martani:

"Na taya ki murna. Ina alfahari da ke yar'uwa."

Michelle Watson:

"Wannan irin hadadden gida na taya ki murna."

Yan kwanaki kafin biki, ango ya fasa auren amaryarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumi ya soke aurensa da wata tsohuwar dalibar jami'ar Abia (ABSU) bayan ya samu labarin mummunan rayuwar da ta yi a baya.

Wata budurwa mai suna Chichi, ta wallafa a manhajar X cewa ya kamata a yi bikin a ranar 23 ga watan Satumba kuma ta shirya halartan wannan biki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel