Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta tsame babban birnin tarayya karkashin jagorancin Nyesom Wike daga asusun Baitul Malin kasa na bai-daya.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da sallamar manyan jami’an hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya.
Wasu mutane uku da ake zargi da sace mazakutar wani mutum a yankin Sabon Garin Nabardo, a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi sun shiga hannun jami'an tsaro.
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta haramta wasu litattafai da ake amfani da su a makarantu. Wadannan sun haɗa da The Queen Primer da A Royal School Series.
Miyagun ƴan bindiga sum halaka wani mutumin da ya je kai kuɗin fansa a jihar Kaduna. Ƴan bindigan sun halaka shi ne bayan ya ƙi yarda su tafi da shi zuwa daji.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tsokaci game da inda Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban hukumar EFCC yake yayin da ya sanar da nadin Ola Olukoyede.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis, ya nada Ola Olukoyede a matsayin wanda zai maye gurbin Abdulrasheed Bawa daga shugabancin hukumar EFCC.
Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a wata kasuwa a jihar Taraba, inda suka halaka mutum biyu har lahira. Ƴan bindigan sun kai harin ne cikin dare.
Wata budurwa ta ɗauki matakin ƙin amsa tayin neman aurenta da saurayin da suke soyayya tare ya yi. Abin da budurwar ta yi ya sosa zukatan mutane sosai.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari