Yakin Isra'ila-Falasdinu: Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza

Yakin Isra'ila-Falasdinu: Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza

  • Dubban mutane fara rige-rige domin tsira da rayukansu bayan sanarwar da sojojin Isra'ila suka yi na ƙaddamar da farmaki a cikin Gaza cikin sa'o'i 24
  • Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa tuni sojojin Isra'ila na ƙasa suka kutsa kai cikin zirin Gaza a wani yunkuri na kakkabe ƙungiyar Hamas mai kishin Islama
  • An tattaro cewa dubunnan Falasdinawa, sun tsere daga arewacin Gaza zuwa yankin Kudancin domin tsira

Gaza, Falasdinu - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa dakarunta na ƙasa sun fara aiki a cikin zirin Gaza.

A cewar Aljazeera, sojojin Isra'ila sun yi gargadi a ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba, inda suka baiwa mazauna yankin sa'o'i 24 su fice daga Arewacin zirin Gaza.

Sojojin Isra'ila sun shiga Gaza
Yan sandan Isra'ila sun kama wani Bafalasdine a Jerusalem a watan Satumban 2017 Hoto: Ilia Yefimovich
Asali: Getty Images

An yi amanna cewa dubban Falasdinawa ne suka tsere zuwa Kudancin zirin Gaza domin neman mafaka a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke da niyyar fara kai farmaki ta ƙasa kan kungiyar Hamas a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai mafi muni a tarihin Isra'ila.

Kara karanta wannan

Bayan Ganin Kamun Ludayin Tinubu, Kiristocin Najeriya Sun Canza Tunani Kan Tikitim Musulmi da Musulmi

A halin da ake ciki dai ana ta mayar da martani a duk duniya dangane da yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga a birnin New York

A wani rahoto da tashar Aljazeera ta fitar a baya-bayan nan, daruruwan mutane ne suka yi dafifi da yawansu domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a birnin New York na ƙasar Amurka.

An ga masu zanga-zangar a cikin adadinsu suna ɗaga tutocin Falasdinawa da alamun da ke cewa "Free Palastine".

An tattaro cewa wasu masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙar cewa gwamnatin Amurka ta daina ba wa sojojin Isra'ila kuɗaɗe.

Saudiyya ta yi kira da a tsagaita wuta

Hakazalika, gwamnatin Saudiyya ta yi kira da a tsagaita buɗe wuta tare da nuna goyon baya ga Falasdinawa.

A babban masallacin Makkah, limamin masallacin Sheikh Osama bin Abdullah Khayyat ya zubar da hawaye yayin da yake jagorantar sallah yana mai cewa: Allah ya kare musulmin Palasɗinu.

Kara karanta wannan

Yakin Isra'ila/Falasdinu: Isra'ila Ta Yi Barazanar Datse Wuta, Ruwa da Fetur Kan Abu 1 Tak, Bayanai Sun Fito

Shehin Malamai Ya Yi Hasashen Rushewar Isra'ila

A wani labarin kuma, sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Mansur Isa Yelwa a wani karatu da ya gabatar ya hasko maganar da wani malamin Falasɗinawa ya taɓa yi a baya.

Marigayi Marigayi Sheikh Ahmad Yasseen ya taba yin hasashen cewa kasar Israila za ta ruguje nan da shekarar 2027 bayan ta balaga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel