Gwamnan Gombe Zai Yi Amfanin Da Kudaden da Ya Kwato Wajen Dankwambo Wajen Biyan Bashin Yan Fansho

Gwamnan Gombe Zai Yi Amfanin Da Kudaden da Ya Kwato Wajen Dankwambo Wajen Biyan Bashin Yan Fansho

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kwato N1.3bn daga hannun tsohon gwamna Dankwambo
  • Gwamna Inuwa ya bayyana cewa an samu nasarar kwato kuɗaɗen ne da taimakon hukumar EFCC
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen ne wajen biyan bashin yan fansho da gratuti

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta taimaka wa gwamnatinsa da jihar wajen kwato N1.3bn daga hannun tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo.

Ya kuma bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen biyan kuɗaɗen fansho da gratuti, da gwamnatocin da suka shuɗe ba su biya ba, cewar rahoton The Punch.

Gwamna Inuwa zai biya yan fansho bashi
Gwamna Inuwa zai biya yan fansho bashin da suke bi Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Gwamna Inuwa ya ce tun hawarsa kan karagar mulki gwamnatinsa ta ƙaddamar da bincike kan gwamnatin Dankwambo bisa zargin karkatar da kuɗaɗe a lokacin da ya ke mulki.

Kara karanta wannan

Kujerar Mataimakin Gwamnan APC Na Tangal-Tangal, Majalisa Ta Tabbatar da Shirin Tsige Shi

Ya ce kawo yanzu binciken da aka gudanar tare da haɗin gwiwar hukumar EFCC ya kai ga kwato N1.3bn da aka karkatar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da a ranar Alhamis yayin rantsar da sabbin kwamishinoni da manyan sakatarori 12 da kuma shugaban ma'aikatan jihar a Gombe.

Gwamna Inuwa ya gaji bashi a Gombe

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji bashi da ya haɗa da maƙudan kuɗaɗen ƴan fanshon da ba a biya ba.

Gwamnan ya cigaba da cewa:

"Mun biya sama da Naira biliyan 7.9 na bashin gratuti da muka gada daga gwamnatin da ta gabata, mun tabbatar da biyan fansho akan lokaci tare da aiwatar da sabon mafi karancin albashi a matakin jiha tun watan Fabrairun 2020."
"Yanzu, bisa jajircewar hukumar EFCC, mun samu nasarar kwato N1.3bn daga hannun Dankwambo, za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen cigaba da biyan kuɗaɗen fansho da garatuti na ma'aikatan mu da suka yi ritaya."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Karbo N41bn, An Fallasa Tsofaffin Jami'an da Ake Bincike a Gwamnati

Gwamna ya kyauta sosai

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gombe mai suna Musa Snai, wanda ya yaba da wannan aikin da gwamnan zai yi.

Ya bayyana cewa tabbas biyan kuɗaɗen ba ƙaramin taimakawa zai yi ba, saboda an daɗe ba a biya ƴan fansho da masu gratuti haƙƙinsu ba a jihar.

Abiodun Ya Shawarci Kwamishinoni

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ogun, ya rantsar da sabbin kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman.

Gwamna Dapo Abiodun ya buƙaci masu sabbin muƙaman da su zage damtse wajen kawo cigaba ga al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel