Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Shugabanni 14 a Ma'aikatar Kasuwanci Da Masana’antu

Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Shugabanni 14 a Ma'aikatar Kasuwanci Da Masana’antu

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin wasu sabbin nade-nade guda 14 a gwamnatinsa
  • Kakakin shugaban kasar ne sanar da sabbin nade-naden a cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba
  • A wannan karon, shugaban kasar ya waiwayi bangarorin kasuwanci, masana'antu da zuba jari ne

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabannin hukumomi da dama a karkashin ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba hannun jari.

Kamar yadda fadar shugaban kasa ta rahoto, hakan ya yi daidai da shawarar da Tinubu ya yanke na farfado da tattalin arzikin Najeriya kan ginshikin fadada kasuwanci ta hanyar inganta kanana, matsakaita da kuma manyan masana’antu a kasar.

Shugaban kasa Tinubu ya yi manyan nade-nade 14
Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Shugabanni 14 a Ma'aikatar Kasuwanci Da Masana’antu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai ne ya sanar da sabbin nade-naden a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Babban Abin Da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi Gabanin Shugaba Tinubu Ya Gama Shekara 8

Sanarwar ta ce nade-naden ya fara aiki nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin sunayen wadanda aka nada a kasa:

  1. Hukumar yiwa kamfanoni Rijista ta kasa (CAC) — Hussaini Ishaq Magaji (SAN)
  2. Hukumar Bunkasa Sarrafa Sukari (NSDC) - Kamar Bakrin
  3. Hukumar horar da sana'o'in hannu (ITF) — Afiz Ogun Oluwatoyin
  4. Hukumar Kula da Fitar da Kayayakin da Ake Samarwa a Cikin Gida (NEPZA) — Olufemi Ogunyemi
  5. Hukumar Bunkasa Sayarda Kayayyakin Najeriya ga Kasashen Waje (NEPC) — Nonye Ayeni
  6. Hukumar Bunkasa Zuba Jari (NIPC) — Aisha Rimi
  7. Hukumar Kula da Yanayin Man Fetur da Gas (OGFZA) — Bamanga Usman Jada
  8. Hukumar kula da ingancin kayayyakin masana'antu ta kasa (SON) — Ifeanyi Chukwunonso Okeke
  9. Hukumar Kula da Bayanan Kudi (FRCN) — Rabiu Olowo
  10. Hukumar bunkasa kananan sana'o'i ta Najeriya (SMEDAN) — Charles Odii
  11. Kasuwar Baje-Koli ta Kasa da ke Legas (LITFCMB) — Veronica Safiya Ndanusa
  12. Hukumar Kula da Dandalin Tafawa Balewa (TBSMB) — Lucia Shittu
  13. Hukumar Kula da Musayar Kayayyaki (NCE) — Anthony Atuche, CFA
  14. Hukumar Bunkasa Kirkira da Zane-Zane (NADDC) — Oluwemimo Joseph Osanipin

Kara karanta wannan

Shin Bawa Ya Yi Murabus Bayan Tinubu Ya Dakatar Da Shi a Matsayin Shugaban EFCC?

KWASU: Shugaba Bola Tinubu ya kuma nada dalibar jami'a a mukami

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa ɗalibar jami'ar jihar Kwara (KWASU), Olamide Obagbemileke, a kwamitin tsare-tsaren kasafi da fasalin haraji.

Ɗalibar 'yar aji huɗu watau 400 Level dai tana karatun ilimin tattalin arziƙi a jami'ar kuma shugaba Tinubu ya naɗa ta a matsayin mai taimaka wa kan bincike da nazari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel