Ola Olukoyede: Abubuwan Sani Dangane da Sabon Shugaban Hukumar EFCC

Ola Olukoyede: Abubuwan Sani Dangane da Sabon Shugaban Hukumar EFCC

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da masu yi wa arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta samu sabon shugaba
  • Ola Olukoyede shi ne mutum na farko wanda ya fito daga Kudancin Najeriya da zai shugabanci hukumar EFCC
  • Olukoyede wanda haifaffen jihar Ekiti ne, ya riƙe muƙamai da dama a hukumar kafin ya kai ga matsayin shugaba

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da masu yi wa arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ne ya sanar da naɗin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Hukumar EFCC ta yi sabon shugaba
Ola Olukoyede ya zama sabon shugaban EFCC Hoto: @Imranmuhdz, @officialBAT.
Asali: Twitter

Ana sa ran Olukoyede zai yi aiki na tsawon shekaru hudu, bayan majalisar dattawa ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar EFCC Wanda Ya Maye Gurbin Bawa

A watan Yunin wannan shekara ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan shugaban ƙasar ya naɗa Abdulkarim Chukkol, wanda a lokacin yake riƙe da muƙamin daraktan ayyuka a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar.

Abubuwan sani dangane da Olukoyede

Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon shugaban na hukumar EFCC:

  • Olukoyede ya fito daga jihar Ekiti, a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, shi ne mutum na farko da ya fito daga Kudancin Najeriya da zai taba riƙe shugabancin hukumar tun bayan kafa ta
  • An haife shi a Ikere-Ekiti a ranar 14 ga Oktoban 1969.
  • Ya yi karatu a jami'a a jami'ar jihar Legas (LASU), Institute of Arbitration - ICC da ke Faransa da kuma jami'ar Harvard.
  • Olukoyede gogaggen lauya ne wanda ke da shekaru sama da shekara 22 na ƙwarewa a fannin.
  • Ya na da ƙwarewa sosai a harkokin hukumar EFCC, inda a baya ya taɓa riƙe mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban hukumar (2016-2018).
  • Babban fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG)
  • Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi sakataren hukumar EFCC (2018-2023)

Kara karanta wannan

Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa

Bawa Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma, dakataccen shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya haƙura da shugabancin hukumar.

Bawa ya yi murabus ne wanda hakan ya bayar da dama a naɗa sabon shugaban hukumar, bayan ya kwashe yana tsare a hannun hukumomi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel