Manyan Labarai A Yau
Wata mata mai ɗauke da juna biyu ta haihu a cikin motar bas lokacin da suke tafiya zuwa birnin Warri, babban birnin jihar Delta a yankin Kudu maso Kudu.
Taron cimma yarjejeniyar zaman lafiya da hukumar INEC ta shirya kan zaɓen gwamnan Imo a birnin Owerri, ya zo ƙarshe cikin rigima a tsakanin jam'iyyu.
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sanya hannu kan karin kasafin kudin N2.17tn na shekarar 2023 a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin rumfunan zaɓe 40 waɗanda ba za a gudanar da zaɓe ba a zaɓen gwamnan jihar Imo na ranar Asabar.
Dama an ce nai son abin ka ya fi ka dabara, Wani 'dan kasuwaya na ji ya na gani, ya hadu da sharrin damfara. Daga gwanji, an yi wa mai mota wayau da rana tsaka
An bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan sukar da wasu ƴan 'Obidients' suka yinwa Peter Obi bayan ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan zaɓen shugaban ƙasa.
Jam'iyyar APC reshen Amurka ta yi Allah wadai da kirayen-kirayen da ake na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus daga kan mulkin ƙasar nan.
Wata mata ƴar Najeriya da suka haɗu da mijin da ta aura a soshiyal midiya ta faɗi yadda haduwarsu ta kaya, inda yanzu sun yi aure bayan abun ya fara kamar da wasa.
An ba Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), shawara guda biyu kan abin da zai yi bayan rashin nasara a kotun koli.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari