Zaben Gwamnan Imo: Da Yiwuwar Ba Za a Yi Zabe Ba Bayan An Samu Sabani Kan Wani Muhimmin Abu 1

Zaben Gwamnan Imo: Da Yiwuwar Ba Za a Yi Zabe Ba Bayan An Samu Sabani Kan Wani Muhimmin Abu 1

  • Rikicin zaben gwamnan jihar Imo na ƙara zafafa wanda zai iya sa a ɗage zaɓen na ranar 11 ga watan Nuwamba
  • Akwai sabanin ra'ayi da rade-radi daga ɓangaren ƴan adawa game da hukumar zaɓen jihar mai zaman kanta
  • Al'amura sun ƙara ta'azzara yayin da taron neman zaman lafiya da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shirya, aka tashi baram-baram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Owerri, Imo - Wani taron zaman lafiya da INEC ta shirya kafin zaɓen gwamnan jihar Imo ya zo ƙarshe cikin ruɗani a Owerri, babban birnin jihar a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Kwamishinan INEC na ƙasa mai wakiltar Kudu maso Gabas, Kenneth Ukeagu, ya umurci ƴan jarida da su kashe na'urorinsu a wajen taron, lamarin da ya janyo tada zaune tsaye.

Kara karanta wannan

"Yana Tunanin Waye Shi?": Ƴan 'Obidients' sun koma caccakar Peter Obi Kan Wani Abu 1

An tashi baram-baram wajen taron zaman lafiya kan zaben Imo
Taron zaman lafiya kan zaben gwamnan Imo ya tashi baram-baram Hoto: Hope Uzodimma/Samuel Anyanwu/Athan Achonu
Asali: Facebook

A yayin zaman tattaunawar ne dai hargitsi ya ɓarke yayin da mahalarta taron musamman sarakunan gargajiya suka yi gaggawar ficewa daga wurin taron sakamakon adawar da ƴan jam'iyyar Labour Party da na PDP suka yi na nuna adawa da umarnin Ukeagu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara samun matsala ne lokacin da Ukeagu ya shaida wa manema labarai cewa su kashe kayan aikinsu, matakin da mataimakin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour, Tony Nwulu ya ƙalubalanta, inda ya nuna shakku kan dalilansa.

Ƴan adawa na zargin APC da yin aiki da INEC wajen murɗe zaɓe

Jam’iyyun adawar sun zargi APC da ƙulla makarkashiya da INEC domin yin maguɗin zaɓe, wanda hakan ya kai ga tafka zazzafar muhawara.

Ana cikin zazzafan taron, an tattaro cewa sarakunan gargajiya, shugabannin jam’iyya, da kwamishinonin zaɓe sun fice taron, amma daga baya an cigaba da taron, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Yayin da aka cigaba da taron, jam'iyyun adawa sun dage kan cire kwamishinan zaɓe na jihar, Sylvia Agu, wanda suke zargin yana goyon bayan APC.

Shugabannin jam'iyyar Labour Party sun caccaki hukumar zabe ta INEC saboda rashin cire Sylvia Agu duk da zanga-zangar ƴan adawa.

Daga bisani ƴan takarar gwamna na jam’iyyar adawa sun fice daga taron inda suka yi kira da a gaggauta cire Agu inda suka zargi shugaban INEC, Mahmood Yakubu da yiyuwar aikata rashin ɗa’a.

Nwulu, ɗan takarar mataimakin gwamna na LP, ya ba da shawarar cewa idan Sufeto Janar na ƴan sanda zai iya canja kwamishinan ƴan sandan jihar, ya kamata INEC ta yi haka kan Agu.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ebere Macdonald, ya yi watsi da iƙirarin ƴan adawar da cewa ba shi da tushe balle makama.

Ba Za a Yi Zabe a Rumfuna 40 a Imo Ba

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin rumfunan zaɓe 40 da ba za a gudanar da zaɓe ba, a zaɓen gwamnan jihar Imo.

Hukumar ta bayyana cewa ba za a gudanar da zaɓen ba ne a rumfunan saboda babu masu kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel