Manyan Labarai A Yau
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya buƙaci Shugaba Tinubu da Kashim Shettima su yi murabus daga muƙamansu.
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun halaka mutane masu yawa a wurin wani taron Mauludi a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba ya amince da naɗin sabbin kwamishinoni guda uku da za su yi aiki a hukumar NUPRC.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da aniyarta na aurar da 'yan TikTok na jihar. Daga cikin wadanda za a aurar harda fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya kafa tarihi inda ya ɗauko mace ya naɗa ta a matsayin mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sallami ɗaya daga cikin kwamandajojinta daga aiki saboda haɗa baki da yake yi da masu otal domin aikata baɗala a jihar.
Ƙungiyar SERAP ta yi barazanar shigar da Shugaba Tinubu da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ƙara a gaban kotu saboda dukan da aka yi wa Joe Ajaero.
Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 10 da suka addabi mutane a jihar Kaduna. Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa.
Wata matashiya yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta duba cikin matashin kai da ta siya a wajen wani mallam bahaushe. Ta ce N800 ta biya ya kan shi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari