An Damfari ‘Dan Kasuwa An Sulale da Motar N6m Ana Tsakiyar Gwajin Lafiyar Inji

An Damfari ‘Dan Kasuwa An Sulale da Motar N6m Ana Tsakiyar Gwajin Lafiyar Inji

  • Olatubosun Gafar wani ‘dan kasuwa ne da ya ke harkar motoci, amma ya gamu da sharrin wani ‘dan damfara kwanan nan
  • Wannan mutumi ya na zaune sai wani ya zo da sunan zai saye Toyota Camry 2014, washegari kuwa ya biya kudin motar
  • Sai da wannan ‘dan damfara ya bar shagon da mota, sannan aka gano cewa sakon aika kudin karya ya aikawa mai shago

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wani dillalin mota da aka bada sunan shi da Olatubosun Gafar ya rasa inda zai sa kan shi tun da wani mutumi ya damfare shi.

Abin da ya faru kuwa shi ne Segun Opeyemi ya zo kamar zai saye motarsa, amma a karshe ya yi masa sata, Punch ce ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Ana saura kwanaki 3 zaben gwamna, a karshe tsohon shugaban kasa ya bayyana wanda ya ke muradi

Shi wannan Segun Opeyemi ya aikawa ‘dan kasuwan sakon shigar kudi har N6.2m, wanda sai daga baya aka iya fahimtar cewa na bogi ne.

Mota.
Wata motar Toyota Camry Hoto: www.thecarconnection.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan damfara ya tsere da mota

Wanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki ya shiga ofishin Olatubosun Gafar ne a ranar Laraba da ta wuce, ya ce yana son mota.

Wannan mutumi mai shekara 39 ya nuna ya na sha’awar sayen Toyota Camry kirar 2014 da aka fi sani da Spyder wanda ta ke shagon.

Salon damfara da aka kawo

Washegari watau safiyar Alhamis, sai ya dawo shagon ya kuma biya kudi, ya aika masa da risitin banki ta WhatsApp domin ya shaida.

Bayan ya nuna hujjar biyan kudi, sai ya nemi a ba shi motar ya jarraba ta domin ya cire kudi a wani banki da yake kusa da shagon motocin.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

Har da mai motar aka shiga, amma daga baya sai Opeyemi ya ce zai je wajen mahaifiyarsa domin ta ga sabuwar motar da ya sayo.

Daga nan sai aka bukaci ya koma shago ya karbi risitin lambar motar, amma sai wannan mutumi ya tubure, ya ce tsohuwarsa na jiran shi.

Pulse ta ce Opeyemi ya bada N50,000 na la’ada da lamba. ya roki ya je ya dawo. Sai bayan nan aka je banki, aka gano damfara ce aka yi masu.

Har yanzu ba a sake jin duriyarsa ba, mai shagon ya bayyana cewa ya rasa yadda aka yi aka cuce sa, kudin ba su shiga cikin asusun ba har yau.

Badakalar digiri a LASU

Ana da labari Majalisar dokokin Legas za ta kira shugabannin LASU domin a gano gaskiyar zargin badakalar da ake tafkawa na saida digirin bogi.

Ana zargin cewa idan mutum ya je jami’ar Legas, da ‘yan miliyoyinsa zai iya sayen digirin bog, kudin a ya danganta da wahalar karatun kwas din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel