"Uwa da Ƴa Duk Cikin Ƙoshin Lafiya": Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu Cikin Motar Bas, Bidiyon Ya Yaɗu

"Uwa da Ƴa Duk Cikin Ƙoshin Lafiya": Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu Cikin Motar Bas, Bidiyon Ya Yaɗu

  • Wata mata mai juna biyu ta haifi jariri a cikin wata motar bas ta kasuwanci da ta nufi garin Warri na jihar Delta
  • Wata mata da ta yaɗa hoton bidiyo daga lokacin da aka haifa jaririn ta yi ƙarin haske kan yadda fasinjojin suka yi lokacin haihuwar
  • Masu amfani da yanar gizo sun godewa Allah da ya ba wa jaririyar da mahaifiyarta lafiya yayin da suka yi mamakin faruwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata mata mai juna biyu ta haifi wata jariri a cikin motar kasuwanci da ta nufi garin Warri a jihar Delta.

Mai amfani da TikTok, @estacyc, ta sanya bidiyo kan yadda matar ta haihuwa a TikTok, inda ta yi nuni da cewa da mahaifiyar da abin da ta haifa duk suna raye cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Kamar wasa, wata mata ta koma yin rarrafe a taron biki, bidiyon ya girgiza intanet

Mata mai juna biyu ta haihu cikin motar bas
Mata mai juna biyu ta haihu a cikin motar bas kan hanyar zuwa Warri Hoto: @estacyc
Asali: TikTok

@estacyc taa ƙara da cewa matar ta haifi ɗiya mace kuma fasinjojin sun ji dadin wannan lamarin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Uwa da rai jariri da rai, fasinjoji suna murna." ALLAH YA YI, ƴar kyakkyawar yarinya.'' @estacyc ta rubuta a kan TikTok.

A cikin faifan bidiyon, wata mata a bayan fage ta bayyana cewa matar ta haifi jaririyar cikin sauƙi.

Ƴan soshiyal midiya sun taya ta murna

Babe ta rubuta:

"Omo barka da zuwa mummy V oo, nagode Allah ya bashi nasara, makwabciyata mai kirki."

user4269208030546 ya rubuta:

"Allah mun gode maka da ka sa muka samu daga cikin falalarka."

user5799821023267 ya rubuta:

"Idan namiji ne a sanya masa suna...Carlos idan kuma mace ce...a sanya mata suna Carlista."

Noney_Nwaeurop ta rubuta:

"Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki akan komai."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, sun tafka ɓarna yayin da suka yi garkuwa da mutane

user8266375861487 ya rubuta:

"Allah ya baki lafiya."

Kyakkyawar Mata Ta Sauya Saboda Juna Biyu

A wani labarin kuma, wata kyakkyawar mata ta samu sauyin fasalin halittar ta lokacin da ta samu juna biyu wanda bai wuce watanni biyu ba da shigarsa a jikinta..

Gabadaya fasalin matar dai sun canja kamar ba ita ba duk kuwa da cewa juna biyun na ta ba wani daɗewa ya yi ba da samunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel