Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Amince da Sabbin Nade-Nade 20, Jerin Sunaye
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin kwamishinoni 20 domin aiki a hukumar kidaya ta kasa (NPC)
- Mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa mutanen za su yi aiki a matsayin kwamishinonin tarayya
- Daga cikin kwamishinonin da aka nada akwai guda tara da za su dawo a wa'adi na biyu
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin kwamishinoni 20 domin su yi aiki a hukumar kidaya ta kasa wato NPC.
Tinubu ya yi sabbin nade-naden ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.
![Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin NPC Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin NPC](https://cdn.legit.ng/images/1120/032892523964999c.jpeg?v=1)
Asali: Twitter
Shugaban kasar ya bukaci sabbin kwamishinonin da masu dawowa da su yi nasarar aiwatar da dukkan matakan da gwamnatinsa ta dauka don samar da ainahin bayanan jama'a.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/34636a11fb29f3b0.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa
A cewarsa, da wadannan bayanai ne za a samar da mafita mai dorewa ga matsalolin tattalin arziki da zamantakewa a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan rantsar da shi a watan Mayu, shugaban kasar ya yi nade-nade da dama domin tabbatar da ganin ya cimma muradinsa na sabonta fatan yan Najeriya kamar yadda ya yi alkawari.
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin NPC
- Hon. Emmanuel Trump Eke — Abia
- Dr. Clifford Zirra — Adamawa - An sake nada shi ne
- Mista Chidi Christopher Ezeoke — Anambra - An sake nada shi ne
- Barr. Isa Audu Buratai — Borno - An sake nada shi ne
- Bishop Alex Ukam — Cross River
- Ms. Blessyn Brume-Ataguba — Delta
- Dr. Jeremiah Ogbonna Nwankwegu — Ebonyi
- Dr. Tony Aiyejina — Edo - An sake nada shi ne
- Mista Ejike Ezeh — Enugu - An sake nada shi ne
- Mista Abubakar Damburam — Gombe - An sake nada shi ne
- Farfesa Uba Nnabue — Imo - An sake nada shi ne
- Ms. Sa'adatu Dogon Bauchi Garba — Kaduna
- Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa — Kano
- Hon. Yori Afolabi — Kogi
- Hon. Olakunle Sobukola — Ogun
- Hon. Temitayo Oluseye Oluwatuyi — Ondo
- Sen. Mudashiru Hussain — Osun - An sake nada shi ne
- Ms. Mary Ishaya Afan — Plateau
- Mista Ogiri Itotenaan Henry — Rivers
- Mista Saany Sale — Taraba - An sake nada shi ne
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/7d4db685d1da2d34.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai
Tinubu ya rattaba hannu a kasafin kudi
A wani labarin, mun kawo a baya cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan karin naira tiriliyan 2.17 na kasafin kudin 2023.
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Tinubu ya sanya hannun ne a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng