"Ki Aure Ni": Hoton Hira Ya Nuna Yadda Dan Najeriya Ya Nemi Auren Matarsa, Hotunan Sun Dauki Hankula

"Ki Aure Ni": Hoton Hira Ya Nuna Yadda Dan Najeriya Ya Nemi Auren Matarsa, Hotunan Sun Dauki Hankula

  • Wata mata ta bayyana yadda ta amsa tayin mijinta bayan ya nemi aurenta a shafukan sada zumunta
  • Wani hoton hirarsu da Maryam Pounds ta wallafa a Twitter ya nuna cewa Alhaji Araphat ya nemi aurenta a shekarar 2021
  • Yanzu haka Maryam da Araphat sun yi aure bayan labarin soyayyarsu ya fara kamar wasa a shafin Twitter

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata ƴar Najeriya da ta haɗu da mijinta a kan manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter) ta bayyana hirar da suka fara yi a dandalin sada zumunta.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, matar mai suna Maryam Pounds, ta saka hoton tattaunawar da ta kai ga mutumin nata ya nemi aurenta.

Kara karanta wannan

A shirya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi mamayar da Tinubu zai yi wa 'yan boye dala

Dan Najeriya ya hadu da matarsa a yanar gizo
Abin da ya fara kamar wasa ya kai ga aure a tsakaninsu Hoto: Twitter/@_odessa_.
Asali: Twitter

Lamarin ya fara ne a lokacin da mutumin mai suna Alhaji Araphat ya ce wa Maryam ta aure shi. Hakan sai ya zama kamar wasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, Maryam ta nemi ya kawo zoben sanya rana da kuɗin sadaki. A wata amsa da ya mayar mata, Araphat ya ce mata ta fara amsa tayin da ya yi mata tukunna.

Auren su ya zo bayan abin da ya fara kamar wasa a Twitter. A wata sabuwar wallafa kuma, Maryam ta bayyana yadda zamantakewarsu ke tafiya.

Masu amfani da yanar gizo sun taya su murna

@Fayokunmii ya rubuta:

"Allah ya albarkaci gidanku. Ina taya ku murna."

@homa1204 ta rubuta:

"Allah ya sa albarka a aurenku barakallahu feeh."

@_Rolex523 ya rubuta:

"A'a wasa na kawai na ke a twitter, dubi abokina."

@Ebonygold1645 ya rubuta:

Kara karanta wannan

So gamon jini: Daga yanke mata farce, kyakkyawar budurwa ta fada soyayya da mai yankan kumba

"Kai!!! Wannan yayi kyau sosai na ji muku daɗi sosai. Ina taya ku murna."

@MFTeemah ta rubuta:

"Ina taya ki murna ƴar uwa, Allah ya albarkaci auren ku."

@Ednut_1 ya ce:

"Shin akwai wanda ya lura da saurayin bai ce "Don Allah ki aure ni ba?" Saboda bai kamata ka roƙi mace ta aure ka ba."

Budurwa Ta Nemi Shiga a Wajen Saurayi

A wani labarin kuma, wata budurwa ta cire kunya inda buƙaci wani saurayi da ya ba ta lambar wayarsa.

Budurwar ta bayyana cewa ita ce ta fara nuna tana ciki a lokacin da ta yi arba da shi sannan daga bisani ta nemi ya bata lambar wayarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel