Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Kiraye-Kirayen da Ake Na Shugabba Tinubu Ya Yi Murabus

Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Kiraye-Kirayen da Ake Na Shugabba Tinubu Ya Yi Murabus

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cigaba da samun matsin lamba kan ya yi murabus daga shugabancin Najeriya
  • Jam'iyyar APC reshen Amurka ta yi Allah wadai da waɗannan kiraye-kirayen inda ta ce hakan bai dace ba
  • A cewar jam'iyyar kiraye-kirayen neman ganin Tinubu ya yi murabus cin mutunci ne ga kotun ƙoli da dimokuraɗiyyar ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Amurka - Jam'iyyar APC reshen Amurka a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba, ta caccaki kiraye-kirayen da ake yi na Shugaba Tinubu ya yi murabus, inda ta ce hakan bai dace ba.

Jam'iyyar APC ta Amurka ta yi gargaɗi kan tsangwamar alƙalan kotunan zaɓe da na kotun ƙoli, wanda wasu ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare suka fara, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Kungiyar SERAP za ta shigar da kara kan Shugaba Tinubu da Gwamna Uzodinma kan abu 1

APC ta caccaki masu neman Tinubu ya yi murabus
Jam'iyyar APC ta caccaki masu son Shugaba Tinubu ya yi murabus Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wannan Allah-wadai dai na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da gamayyar ƙungiyoyin ƴan Najeriya 30 suka shirya gudanarwa a ƙarkashin haɗakar 'Coalition of New Nigeria Diaspora Movement' ta neman shugaban ƙasar ya yi murabus cikin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakatare Janar na ƙungiyar, Jackson Ude, yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, ya roki ƙungiyar Tarayyar Turai, Birtaniya da Amurka da su sanya takunkumin biza ga dukkanin alƙalan kotun zaɓe da kotun ƙoli waɗanda suka tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu.

Wane martani jam'iyyar APC ta yi?

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 7 ga watan Nuwamba, shugaban jam’iyyar APC ta Amurka, Farfesa Tai Balofin, ya bayyana zanga-zangar a matsayin abin da ya saɓawa doka.

Balofin ya kuma bayyana matakin a matsayin wulakanci ga kotu, wanda ya ce ya taɓa ƙima da martabar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Ba zan taba daina kiran Tinubu dillalin kwayoyi ba", Datti Baba-Ahmed ya bayar da dalili

Yayin da ta ke nuni da cewa zanga-zangar ta nuna rashin muhimmancin bin ƙa’idojin doka, jam’iyyar APC ta Amurka ta jaddada cewa yana da matukar muhimmanci a mutunta hukuncin kotun ƙoli.

Jam'iyyar ta yi nuni da cewa hukuncin kotun ƙoli ba abin da za a tsaya jayayya a kansa ba ne ko ƙin mutunta shi, saboda kaucewa kawo cikas ga tushen tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Datti Na Son Tinubu da Shettima Su Yi Murabus

A wani labarin kuma, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed ya buƙaci Shugaba Tinuɓu da Kashim Shettima su yi murabus.

Datti ya yi nuni da cewa rantsuwar da aka yi wa shugabannin biyu ta saɓa kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel