Manyan Labarai A Yau
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya bayyana cewa Nyesom Wike zai hana Gwamna Fubara na Rivers sakat.
Dakarun sojoji a jihar Taraba sun samu nasarar fatattakar wasu miyagun ƴan ta'adda masu yin garkuwa da mutane. Sojojin sun kuma ceto mutanen da suka sace.
Oba Ewuare II na Benin ya bayyana cewa Allah yana goyon bayan shugabancin Bola Tinubu. Basaraken ya bukaci yan Najeriya da su mara wa gwamnatinsa baya.
Rahotanni sun nuna cewa goba ta tashi a babbar kasuwar Kabba da ke jihar Kogi, inda ta lakume shaguna masu tarin yawa. An yi asarar dukiya mai tarin yawa.
Oba Saheed Ademola Elegushi ya shawarci mutanensa da su daina amfani da itace saboda gurbata muhalli yayin da ya raba musu tukunyar iskar gas domin yin girki.
Farfesa Farouq Kperogi ya yi bayanin dalilin da ya sanya Peter Obi da Atiku Abubakar suka kasa yin nasara a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kotu.
Wata kungiya ta matasan Najeriya ta yi kira ga hukunta Atoni Janar na jihar Kano kan firucinsa na zargin bangaren shari’a da aikata rashawa a hukuncin zaben Kano.
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana crwa matatar man fetur ɗinsa ta shirya fara aiki a cikin watan Disamba kamar yadda aka tsara.
Lauyan kare hakkin dan Adam Enibehe Effiong ya yi magana kan dalilin da ya sanya Gwamna Abba Kabir Yusuf da Caleb Mutfwang suke da hujja a kotun koli.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari