Manyan Labarai A Yau
An samu asarar rayukan mutum takwas a wani hatsarin mota da ya ritsa da wasu motoci guda biyu. Motocin sun yi arangama ne a kan wani titin jihar Kwara.
Fasto David Ayuba Azzaman ya bayyana cewa an nuna masa cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu akwai wanda ke juya akalarta a cikin wani wahayi da ya samu.
Dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya shiga sahun yan siyasa wajen taya Atiku Abubakar murna yayin da ya cika shekaru 77 a duniya. Ya kira shi da babban yayansa.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya haƙiƙance cewa shi cikakken ɗan ƙabilar Ijaw wanda ba ya shakkar kowane irin ƙalubale da ya same shi.
Bola Tinubu ya magantu kan rahotannin da ke cewa watakila ya umarci yan majalisar jihar Ondo da su ayyana mataimakin Rotimi Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna.
Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram a wani hari a jihar Borno.
Wani dan Najeriya da ke aiki a matsayin dan agaji ya baje kolin makudan kudaden da yake samu a kullun bayan kula da wani tsoho. Ya ce aikin na ci sosai a Birtaniya.
An samu asarar rayuka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba yayin da wasu miyagun ƴan bindiga, suka kai mummunan farmaki kan wasu ƙauyuka a jihar Taraba.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin Legas ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Manyan Labarai A Yau
Samu kari