Daga Karshe An Bayyana Dalilin da Ya Sanya Atiku da Peter Obi Suka Kasa Yin Nasara Kan Tinubu a Kotu

Daga Karshe An Bayyana Dalilin da Ya Sanya Atiku da Peter Obi Suka Kasa Yin Nasara Kan Tinubu a Kotu

  • Farooq Kperogi, ya ce ko da a ce ɓangaren shari’a sun yi watsi da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu, ba za a ayyana Atiku ko Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaɓe ba
  • Atiku, jigo a jam'iyyar PDP, ya samu kaso 25% ko fiye da haka na ƙuri'u a jihohi 21 a zaɓen da aka gudanar a watan Fabrairun 2023
  • Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne kuma ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP), ya samu kaso 25% ko fiye da haka a jihohi 16 da babban birnin tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja -Farfesa Farooq Kperogi ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka, ya yi magana kan rashin nasarar Atiku Abubakar da Peter Obi kan Shugaba Tinubu a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Farfesan ya ce ko da a ce ɓangaren shari'a ya yi watsi da nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu, babu ɗaya daga cikin Atiku Abubakar ko Peter Obi da ya cancanci a ayyana shi a matsayin shugaban ƙasa.

Kperogi ya yi magana kan shari'ar zaben shugaban kasa
Kperogi ya ce Atiku da Peter Obi ba su cancanci nasara kan Tinubu a kotu ba Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Da yake rubutu a shafinsa na mako-mako a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, Kperogi ya ce Atiku da Obi ba su samu kaso 25% na ƙuri’u a jihohi 24 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan adawa ba za su iya kayar da Tinubu a kotu ba?

A watan Oktoba ne kotun ƙoli ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen ƴan adawa kan nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa.

Tun da farko dai kotun sauraron kararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu.

Da yake sake magana kan lamarin, Farfesa Kperogi ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya bayyana mutum 1 mai juya akalar gwamnatin Tinubu

"Ko da a ce ɓangaren shari'a ya yi watsi da nasarar Tinubu, da ba ko ɗaya daga cikin Atiku ko Peter da a kundin tsarin mulki ya cancanci a ayyana shi a matsayin shugaban ƙasa saboda ba su samu kaso 25% na ƙuri'u ba a jihohi 24."
"Atiku ya samu kaso 25% ko fiye da haka na ƙuri'u a jihohi 21 yayin da Peter Obi ya samu kaso 25% ko fiye da haka a jihohi 16 da birnin tarayya Abuja."

Yadda PDP Za Ta Kwaci Mulki a Hannun APC

A wani labarin kuma, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya ba jam'iyyar PDP shawara kan yadda za ta ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC.

Babban faston ya bayyana cewa dole sai jam'iyyar ta magance rikicin cikin gidan da take fama da shi tare da samun haɗin kai, kafin ta iya karɓe ragamar mulkin ragamar ƙasar nan a hannun APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng