Gwamnan APC a Arewa Ya Hana Amfani da Hijabi a Jiharsa? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan APC a Arewa Ya Hana Amfani da Hijabi a Jiharsa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Neja ta fito ta musanta batun cewa tana adawa da sanya Hijabi da musulmai mata ke yi a jihar
  • Gwamnatin a wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta adawa da sanya Hijabi ba kuma za ta taɓa yi ba
  • A cikin sanarwar gwamnatin ta yi nuni da cewa sanya Hijabi dokar addini ce wacce kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya tabbatar da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, na jam'iyyar APC ya ce jihar ba ta adawa da sanya hijabi da mata musulmai ke yi.

Bago yana mayar da martani ne kan wani rahoto da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke iƙirarin cewa kwamishiniyar ilimi ta jihar, Hajiya Hadiza, ta yi Allah-wadai da sanya Hijabi da malamai mata ke yi, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

APC ta mayarwa Sule Lamido martani: Har yanzu kura-kuren PDP muke gyarawa

Gwamna Bago ya yi magana kan hana sanya Hijabi a Neja
Gwamna Bago ya ce jihar Neja ba ta adawa da sanya Hijabi Hoto: Umaru Bago
Asali: Facebook

A cikin rahoton an yi zargin ta ce ba ta ga dalilin da zai sa wata malama mace za ta sanya Hijabi kuma ta samu natsuwa a yayin da take koyarwarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me nene matsayar gwamnatin kan hana amfani da Hijabi?

Gwamnan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Bologi Ibrahim, ya ci gaba da cewa gwamnatin sa ba ta adawa da sanya Hijabi domin dokar addini ce wacce ke da goyon bayan kundin tsarin mulki.

A cewar Ibrahim, ba a fahimci kalaman kwamishiniyar ba ne, kuma a matsayinta na musulma ba za ta taɓa yin maganar za ta taɓa mutuncin Hijabi ba, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Maganar kwamishiniyar ba a fahimce ta ba kuma baya nuna matsayin gwamnatin jihar kenan kan amfani da hijabi da mata ke yi a kowane fanni na aiki."

Kara karanta wannan

Kaciyar mata: Gwamnan PDP ya haramta al'adar a fadin jiharsa, an bayyana illarta ga mata

"Gwamnatin jiha ba ta adawa da sanya Hijabi, kuma ba ta taɓa yi ba, dole an yi kuskuren fahimtar maganar kwamishiniyar."
"Jihar Neja jiha ce mai bin doka da oda. Tunda kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince ɗalibai da malamai musulmai su riƙa sanya Hijabi, gwamnatin jiha tana da alhakin tabbatar da cewa an kare ƴancin jama'a."

An Hana Dalibai Sanya Hijabi a Makarantun Gwamnati

A wani labarin kuma, gwamnatin ƙasar Faransa ta haramtawa ɗalibai musulmai sanya Hijabi a makarantun ƙasar.

Gabriel Attal, ministan ilmi na ƙasar Faransa ya bayyana hijabi a matsayin wata alamar addini ce wacce take kawo barazana ga tsarin kafa makarantu kan yi wa kowane addini adalci

Asali: Legit.ng

Online view pixel