Malamin Addini Ya Dira a Kan Masu Wa'azi Mata da ke Watsi da Sha’anin Mazajensu Suna Yawon Duniya

Malamin Addini Ya Dira a Kan Masu Wa'azi Mata da ke Watsi da Sha’anin Mazajensu Suna Yawon Duniya

  • Fasto Mike Bamiloye ya yi karin bayani game da wasu rukunin malaman addini mata da ake jin su a duniya amma suka yi watsi da hakokinsu na gida
  • Malamin addinin ya bayyana cewa malaman na yawan tafiye-tafiye saboda ayyukan Allah, suna masu barin mazajensu a gida su kadai na tsawon lokaci
  • Yadda malamin ya jaddada bacin rai kan abun da malaman mata ke yi na yabon mazajensu a kan mimbari yayin da mazajen ke zaman kadaici a gida ya haddasa cece-kuce

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mike Bamiloye, wanda ya kafa cocin Mount Zion Faith Ministries, ya caccaki malaman addini mata wadanda ke yawon zuwa ko'ina amma suna bar wa yan uwa da masu aiki gidaje da mazajensu.

Kara karanta wannan

Babu 'yancin yin haka, malamin addini ya gargadi masu tare hanya don yin salla, an yada bidiyon

Malamin addini ya caccaki masu wa'azi mata
Malamin Addini Ya Dira a Kan Malaman Addini Mata da ke Watsi da Sha’anin Mazajensu Hoto: Mike Bamiloye
Asali: Facebook

Mike Bamiloye ya caccaki malamai mata

A wata wallafa da ya yi a Facebook a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, malamin kuma mai shirya fina-finai ya jaddada cewar malaman na yawon duniya, sannan suna wa'azi. Suna samun kulawa ta musamman yayin aikinsu na duniya amma sun bar mazajensu a gida su kadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Bamiloye ya rubuta:

"Akwai rukunin mata masu wa'azi wadanda basa taba zama a gida tare da mijinsu. Suna yawo ko'ina, ana yi masu masauki a otel-otel a fadin ko'ina yayin da suke wa'azi, suna cin abinci mai rai da lafiya da masu masaukinsu suka tanadar masu yayin da maajensu ke gida su kadai.
"Za su hau saman mumbari tare da fara wa'azinsu da yabon mazajensu: "Na kawo maku gaishuwa da wajen mijina, mamallakina. Wanda ya biya sadakina wanda ba don da shi ba da ba zan kasance a nan ba a yau. Yana aika sakon gaisuwarsa", duk da mutumin yana nan yana fama da kadaici a gida. Cikin sanyi ko zafi mutumin na nan shi kadai."

Kara karanta wannan

Malamin addini ya dira kan mata da ke hana mazajensu hakkin kwanciyar aure, ya fadi halayensu

Jama'a sun yi martani

King Goodluck II ya rubuta:

"Wannan sakon na da zurfi yallabai.
"Allah, ka sa na auri macen da ta dace."

Emmanuel Nyeche ya ce:

"Akwai bukatar a gaggauta gyara wannan."

Victoria Adebo ta ce:

"Ya kamata mutumin ya boye fasfot din sannan ya sa ta dunga neman shi. Hikima na da riba."

Peace Nzewuji ta ce:

"Magana ta gaskiya yallabai."

Malamin addini ya caccaki mata

A wani labarin, mun ji cewa shahararren Fasto a Najeriya, Mike Bamiloye ya caccaki mata musamman Kiristoci da ke hana mazajensu jin dadin kwanciyar aure.

Bamiloye wanda shi ne shugaban cocin Mount Zion Faith ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Asabar 25 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel