Dangote Ya Yi Magana Kan Ranar Fara Aikin Matatar Man Fetur Dinsa, Ya Fadi Abin da Za Ta Fara da Shi

Dangote Ya Yi Magana Kan Ranar Fara Aikin Matatar Man Fetur Dinsa, Ya Fadi Abin da Za Ta Fara da Shi

  • A ƙarshe dai matatar man Dangote za ta fara aiki a watan Disamba kamar yadda aka tsara a baya
  • Dangote ya tabbatar da hakan yayin wata hira da jaridar Financial Times a ranar Asabar, 25 ga Nuwamba, 2023
  • Ya ce an shawo kan dukkanin ƙalubalen da aka fuskanta wajen fara samar da man fetur a matatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote ya tabbatar da cewa matatarsa ​​mai ƙarfin tace litar ɗanyen man fetur 650,000 ta shirya tsaf domin fara tace man fetur na farko a cikin watan Disamba.

Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa, burin farko shine a samar da ganga 350,000 na man fetur a kullum daga matatar man.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da jin jiki a Najeriya, Sanata Yari ya ware 'yan Zamfara 1000 zai tallafa musu da magani

Matatar man Dangote za ta fara aiki
Dangote ya ce matatar man fetur dinsa za ta fara aiki a Disamba Hoto: Bloomberg/Creditor
Asali: UGC

Dangote ya bayyana ƙalubalen fara samar da man fetur

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da Financial Times a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matatar wacce ta gaza fara aiki a lokacin da aka tsara har sau biyu, za ta fara ne da ganga 350,000 a kowace rana, inda ya ce tuni aka cimma matsaya kan fara jigilar ɗanyen mai kusan ganga miliyan shida a watan Disamban 2023.

A kalamansa:

"Za mu fara da ganga 350,000 a rana, ban sani ba ko wasu mutane za su iya tsira idan suka fuskanci irin ƙalubalen da muka fuskanta."
"Ko dai mu gaza ne ko kuma mu yi nasara. Kuma muna godiya ga Allah da ya sa muka isa wurin da aka nufa."

Dangote ya bayyanawa masu zuba jari a ƙasar Saudiyya a wata ziyarar da ya kai ƙasar tare da shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa matatar ta na son ta fara aiki da ɗanyen mai daga kamfanin mai na NNPC.

Kara karanta wannan

Juyin mulki a kasar Saliyo? Abin da muka sani yayin da gwamnati ta sanya dokar hana fita

Matatar ta yi odar gangar danyen mai miliyan shida daga NNPC

An samu rahotannin cewa matatar ta yi odar ɗanyen man fetur ganga miliyan shida daga NNPC, jimillar ganga 200,000 a kullum.

Dangote ya shaidawa jaridar Financial Times cewa ya yi amanna cewa matatar za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana nan da ƙarshen shekarar 2024.

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirika ya ce matatar ta samu nasarar magance duk wasu ƙalubalen da suka shafi samar da ɗanyen mai, inda ya ce a ƙarshe za a sanya ta kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Legas.

Dangote Zai Siyar da Jirginsa

A wani labarin kuma, hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika ya shirya siyar da katafaren jirginsa na alfarma da ya siya domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya biya dala miliyan 45.5 don mallakar jirgin mai zaman kansa a shekarar 2009 (shekaru 13 da suka gabata), lokacin da yake bikin cika shekaru 53 da haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel