Kano: Sakaci da Dokar Zabe Ya Jefa Gwamna Abba da NNPP Cikon Matsala, Kungiya ta Bayyana

Kano: Sakaci da Dokar Zabe Ya Jefa Gwamna Abba da NNPP Cikon Matsala, Kungiya ta Bayyana

  • Ana ci gaba da sukar gwamnatin jihar Kano wacce jam’iyyar NNPP ke jagoranta
  • An caccaki Gwamna Abba Yusuf da jam’iyyarsa kan sakacinsu a zabe da kuma kokarin shafawa bangaren shari’a bakin fenti
  • An kuma bukaci a hukunta Atoni Janar na jihar Kano kan harin da ya kai wa bangaren shari’a

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, AbujaWata kungiyar matasa karkashin inuwar NYP ta caccaki gwamnatin jihar Kano wacce jam’iyyar NNPP ke jagoranta.

An caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf ne kan yadda ta yi watsi da dokokin zabe da gangan game da zaben yan takara.

Kungiya ta caccaki gwamnatin Abba Gida Gida
Kano: Sakaci da Dokar Zabe Ya Jefa Gwamna Abba da NNPP Cikon Matsala, Kungiya ta Bayyana Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Kungiyar ta NYP ta bayyana cewa maimakon kokarin bata sunan bangaren shari’a, kamata ya yi ace gwamnatin NNPP ta dauki alhakin matsalolin da ta janyo wa kanta, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiya ta nemi kungiyar NBA ta sanyawa Atoni Janar na Kano takunkumi

Bugu da kari, kungiyar ta bukaci kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) da ta dauki mataki a kan Atoni Janar na jihar Kano kan zargin da ya yi da kuma wasu kalamai marasa tushe dangane da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a Kano.

Shugaban kungiyar, Kwamrad Magaji Alidu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba.

Alidu ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam'iyyar NNPP sun yi watsi da wani muhimmin bangare na tsarin zabe don haka ya kamata su fuskanci sakamakon sakaci da suka yi.

Ya ce:

“Sashi na 177, karamin sashi na C na kundin tsarin mulkin 1999, wacce aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana cewa dole ne mutum ya kasance dan jam’iyya mai rijista kuma sannan wannan jam’iyyar ta dauki nauyinsa domin ya cancanci tsayawa takarawa kujerar gwamnan wata jiha.

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

“Wannan don nuna cewa ya zama dole masu sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa wata don samun tikitin takara su yi taka-tsan-tsan saboda akwai doka kan haka. Ba Abba Yusuf bane mutum na farko, kuma ba shine zai zama na karshe ba.”

Kungiyar ta kuma nuna takaicinta cewa Atoni Janar na jihar Kano, wanda yake lauya, ya shiga sahun masu bata sunan alkalai da suka yanke hukunci kan karar zaben gwamnan jihar Kano da aka daukaka.

Kungiyar matasan ta ce:

“Irin wannan sam bai dace ba kuma yana bukatar kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta dauki matakin gaggawa don dawo da martabar bangaren shari’a."

An nemi a kama Atoni Janar na Kano

A wani labari makamancin wannan, kungiyar fafutukar tabbatar da adalci da shugabanci na gari (AJGG) ta nemi a gurfanar da Atoni Janar na jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, Barista Haruna Isa Dederi.

Wannan kiran martani ne ga zargin rashawa da Dederi ya yi wa alkalan kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel