Abdul Amart da Rarara Sun Yi Wa Iyalan Marigayi Aminu S Bono Sha Tara Ta Arziki

Abdul Amart da Rarara Sun Yi Wa Iyalan Marigayi Aminu S Bono Sha Tara Ta Arziki

  • Yan masana'antar Kannywood sun shirya taron addu'o'i ga marigayi darakta Aminu S. Bono
  • Shugaban Abnur Entertainment kuma furodusa, Abdul Amart ya mallakawa iyalan marigayin gida a unguwar Dandago da ke garin Kano
  • Haka kuma, fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya dauki nauyin karatun yaran S, Bono

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Babban furodusa a masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Abdul Amart Mohemmed, ya siyawa iyalan Marigayi Aminu S. Bono gida a yayin da kudin hayarsu ke gab da karewa.

Mujallar Fim ta rahoto cewa an siya masu gidan ne a unguwar Dandago da ke garin Kano kan farashi naira miliyan 4.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da mutane 8 da ya naɗa, ya shiga taro da manyan jiga-jigai a Villa

An siyawa iyalin Aminu S Bono gida
Abdul Amart da Rarara Sun Yi Wa Iyalan Marigayi Aminu S Bono Sha Tara Ta Arziki Hoto: @abdulamart_mai_kwashewa/aminusbono/daudakahuturarara
Asali: Instagram

Kamar yadda aka bayyana, Shugaban kungiyar daraktocin Kannywood, Malam Aminu Saira, ne ya sanar da labarin sayen gidan a lokacin da yake jawabi a taron addu'ar bakwai ta marigayi daraktan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abokan sana'ar S. Bono ne suka gudanar da taron addu'ar a majalisar matasa ta Tarauni da unguwar Gyadi-Gyadi a garin Kano, a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba.

Jaridar Aminiya ta nakalto Abdul Amart yana cewa:

“Mutum ne (Bono) da ya kamata tsakani da Allah mu tsaya masa, mu tabbatar ‘ya’yansa sun taso cikin aminci, shi ne karshen kauna da za mu iya nuna masa.
“A shawarce, sai na ce a nemo gida a kusa da gidan iyayensa, Allah kuma cikin ikonsa, ban shirya ba, Allah Ya taimake ni na yi wannan abun."

Mawaki Rarara ya dauki nauyin karatun 'ya'yan Aminu S. Bono

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Hakazalika, shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu wanda aka fi sani da Rarara shima ya bayar da gudunmawarsa ga iyalan marigayi S. Bono.

Yayin da ya ziyarci iyalin a ranar Litinin domin yi masu ta'aziyyar, Rarara ya bayyana aniyarsa na daukar nauyin karatun yaran marigayin daraktan.

Rarara da jama'arsa sun ziyarci iyayen marigayin tare da yi masa addu'o'i sannan daga nan suka isa gidan iyalinsa.

Kamar yadda Mujallar Fim ta rahoto, Aminu S. Bono yana daga cikin daraktocin da Rarara ke aiki da su, musamman a yayin da zai shirya bidiyon wata waka.

Marigayin na cikin wadanda mawakin ya yi wa kyautar motoci a shekarun baya.

Aisha Humaira zata saukewa Bono nauyi

A wani labarin, mun ji a baya cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Aisha Humairah ta dauki nauyin biyawa marigayi Aminu S. Bono duk bashin da ake binsa.

Jarumar ta kuma sh alwashin nema masa taimako a wajen wadanda ya dace idan har bashin da ake binsa ya fi karfinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel