Manyan Labarai A Yau
Wani malamin addini mazaunin Abuja, Fasto Joshua Iginla ya yi hasashen abun da zai faru a shekarar 2024. Malamin addinin ya ce abun zai ba mutane mamaki.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sanar da gwamnatin Tinubu cewa a shirye yake ya bayar da shaida kan Olu Agunloye wanda ake nema ido rufe kan zamba.
Babban lauya Femi Falana (SAN) ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Rivers. Falana ya fadi makomar yan majalisar da suka koma APC.
Sabanin yadda ake ta yada jita-jita a shafukan sada zumunta, jam’iyyar LP ba ta nemi babban jigon ta, Peter Obi ya nemi afuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Bankin duniya ya ce bude kofa domin shigo da kaya kamar shinkafa zai taimaka. Hakan zai sa a fito da mutane miliyan 1.3 daga cikin talauci da ake fama da shi.
Yan bindiga sun aikata barna a Abuja bayan sun sace shugaban kungiyar dillalan jaridu ta birnin tarayya Abuja. Miyagun yan bindigan sun bukaci a ba su N15m.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Simon Bako Lalong, ya shirya yin murabus daga mukaminsa. Ministan zai koma kujerarsa ta Sanata a majalisar dattawa.
An samu tashin gobara har sau biyu a jihar Kwara. Gobarar wacce ta tashi daban-daban a rukunin shagunan ta kona shaguna guda 17 da lalata dukiyoyi.
Majalisar dokokin jihar Ondo ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin mukaddashun gwamnan jihar biyo bayan jinyar rashin lafiyar da Gwamna Rotimi ya koma.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari