Dan Majalisar Dokokin Rivers Mai Biyayya Ga Wike Ya Yi Magana Kan Komawa PDP Bayan Ya Koma APC

Dan Majalisar Dokokin Rivers Mai Biyayya Ga Wike Ya Yi Magana Kan Komawa PDP Bayan Ya Koma APC

  • Tonye Adoki ya yi magana dangane da rahotannin komawar sa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Rivers
  • A yayin da ake cikin guguwar sauya sheka da ya rutsa da jam’iyyar PDP a jihar Rivers a ranar Litinin, ɗan majalisar ya bayyana cewa ba shi da niyyar komawa PDP
  • Adoki ya cigaba da cewa shi ne ya goyi bayan sauya sheka da manyan ƴan PDP suka yi zuwa APC kuma ba ya neman yafiyar kowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Tonye Adoki, daya daga cikin jiga-jigan ƴan majalisar dokokin Rivers da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP kwanan nan ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya koma tsohuwar jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

PDP ta samu gagarumin nasara yayin da tsohon jigon APC ke shirin komawa jam'iyyar

Adoki ya yi magana kan komawa PDP
Adoki ya musanta komawa PDP bayan ya tsallaka APC Hoto: Tonye Adoki, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Adoki ya musanta iƙirarin komawa PDP

Idan dai za a iya tunawa Adoki da wasu mambobi 26 na majalisar mai wakilai 32 sun sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ne dalilin da ya sa suka ɗauki matakin komawa APC.

Ƴan tawagar Edison Ehie da Gwamna Siminalayi Fubara ke marawa baya sun bayyana kujerun mambobi 27 da suka sauya sheƙa a matsayin babu kowa a kansu a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba.

Wasu rahotanni sun bayyana a shafukan sada zumunta na cewa Adoki ya koma PDP.

Sai dai a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Adoki mai wakiltar mazabar Port Harcourt II a majalisar ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Rivers: Jigon APC ya yi wa Gwamna Fubara wankin babban bargo

Wacce rawa ya taka a komawar ƴan majalisar APC?

Sai dai, ya yi nuni da cewa shi ne ya assasa ficewar ƴan majalisar na PDP kuma bai yi nadamar matakin da ya ɗauka ba.

Adoki ya ce:

"Na sani cewa ana amfani da wasu matasa marasa aikin yi da ɓata gari wajen yaɗa labaran ƙarya cewa ni Hon. Tonye Adoki na janye daga yunƙurin sauya sheƙa na."
"A bayyane yake cewa ina cikin ƴan majalisar da suka bayar da shawarar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress kuma ba mai bi na bashin ba da haƙuri."
"Kuma har yanzu ni ɗan APC ne."

FG Ta Yi Magana Kan Rikicin Fubara da Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatim tarayyar Najeriya ta yi magana kan rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa babu hannunta a rikicin wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a tsakanin manyan ƴan siyasar guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel