Rikicin Rivers: Falana Ya Bayyana Abin da Zai Faru da Yan Majalisar da Aka Kora

Rikicin Rivers: Falana Ya Bayyana Abin da Zai Faru da Yan Majalisar da Aka Kora

  • Majalisar dokokin jihar Rivers ta samu kanta cikin rikici bayan wasu mambobin majalisar sun koma APC
  • Femi Falana a wata tattaunawa a baya-bayan nan, ya yi cikakken bayani kan abin da zai faru ga ƴan majalisar da suka fice daga PDP suka koma APC
  • Falana ya ƙara da cewa ƴan majalisar da ke biyayya ga Nyesom Wike ba su da fahimtar doka kan abin da zai same su nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Babban Lauyan Najeriya, SAN, kuma lauyan kare haƙƙin bil'adama, Femi Falana, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Rivers.

Babban lauyan ya ce ƴan majalisar dokokin jihar Rivers da aka ayyana kujerunsu matsayin babu kowa, ba su samu kwakkwarar shawarar doka ba.

Kara karanta wannan

Babban ministan Shugaba Tinubu zai yi murabus, bayanai sun fito

Falana ya yi magana kan rikicin Rivers
Femi Falana ya yi magana kan rikicin siyasar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Femi Falana
Asali: Facebook

Falana ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba 13 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Falana ya ce kan rikicin?

A cewar babban lauyan, doka ta buƙaci hukumar INEC ta gudanar da zaɓe a kujerun ƴan majalisar, kuma da zarar kotun ƙoli ta yanke hukunci kan ko wane irin lamari to magana ta ƙare kuma dole ƴan majalisar su yarda da hukunci, cewar jaridar Vanguard.

Ya ƙara da cewa ayyana kujerun ƴan majalisar da suka sauya sheka a matsayin waɗanda ba kowa a kansu, ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Falana ya bayyana kamar haka:

"Ba a ba ƴan majalisar ingantattun shawarwarin doka ba. Ya kamata kowa ya sani cewa da zarar kotun ƙoli ta yanke hukunci a kan wani lamari a kowace ƙasa, to lallai ne a bi, kuma idan za a ɗauki wani mataki, dole ne a yi nazarin hukuncin cikin tsanaki."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kitsa rikicin Wike da Gwamna Fubara? Gaskiya ta bayyana

"Kotu ta ayyana kujerun ƴan majalisar da suka sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC matsayin waɗanda babu kowa. Wannan ita ce doka, sai dai idan kotun koli ta yanke hukuncin sauya ta, wannan ita ce doka a Najeriya a yau."

FG Ta Magantu Kan Rikicin Siyasar Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta tsame hannunta kan rikicin siyasr da ke aukuwa a jihar Rivers.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da hannu a rikicin siyasar da ya ƙi ya ƙi cinyewa tsakanin Gwamna Fubara da Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel