PDP Ta Samu Gagarumin Nasara Yayin da Tsohon Jigon APC Ke Shirin Komawa Jam’iyyar

PDP Ta Samu Gagarumin Nasara Yayin da Tsohon Jigon APC Ke Shirin Komawa Jam’iyyar

  • Abubuwa sun kammala yayin da shahararren dan kasuwa kuma dan siyasa, Shina Peller, ke shirin hadewa da jam'iyyar PDP
  • PDP ce jam'iyya mai mulki a Oyo, daya daga cikin jihohi biyu da take jan akalarsu a yankin kudu maso yamma
  • Koda dai Petller ya kasance dan APC a farkon shigarsa siyasa, yanzu haka jigo ne a jam'iyyar Accord Party

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Iseyin, jihar Oyo - Shina Peller, tsohon dan majalisar wakilai, yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Oyo.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, Michael Ogunsina, kakakin PDP a jihar ta kudu maso yamma ne ya tabbatar da lamarin.

Kara karanta wannan

"Ina da tarin ilimi": Tsohon shugaban daliban jami'ar UNIBEN ya tsaya takarar gwamna a jihar Edo

Shina Peller na shirin komawa PDP
PDP Ta Samu Gagarumin Nasara Yayin da Tsohon Jigon APC Ke Shirin Komawa Jam’iyyar Hoto: @ShinaPeller
Asali: Twitter

Shina Peller zai bar jam'iyyar Accord Party

Ogunsina ya bayyana cewa tuni aka fara shirye-shirye don shirga ma Peller da magoya bayansa a fadin kananan hukumomi 13 na yankin Oyo ta arewa gagarumin bikin maraba da zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogunsina ya ce:

“Muna farin cikin yiwa Hon. Shina Peller maraba da zuwa jam'iyyar PDP. Irin nasarorin da ya samu da kuma sadaukarwar da yi a aikin gwamnati zai taimaka wajen ci gaban jam’iyyar da kuma burinmu na tabbatar da ci gaban jihar Oyo.”

An zabi Peller a 2019 don ya wakilci mazabar Kajola/Iwajowa/Iseyin/Itesiwaju a majalisar wakilai amma ya bar APC a 2022 gabannin babban zaben 2023 sannan ya yi takarar zaben sanata karkashin inuwar Accord Party.

Ya yanke shawarar barin jam'iyyar APC bayan ya fadi zaben fidda gwani inda ya sha kaye a hannun Abdulfatai Buhari.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

Zamanin da Peller ke APC

Peller ya yi martani kan kayen da ya sha a zaben fidda gwani na sanatan APC a Oyo ta Arewa.

Peller ya sha kaye a zaben fidda gwani a hannun Buhari, wanda ya samu kuri'u 570 yayin da Peller ya samu kuri'u 5.

Ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin sannan ya bayyana cewa APC bata gudanar da kowani zabe ba a Oyo ta Arewa.

Jigon PDP ya koma APC a Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa jigon jami'yyar PDP a jihar Kaduna, Usman Ibrahim ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Usman wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya yi takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel