Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan kudin karatun daliban da ke karantar ilmin da ya shafi karatun lafiya a Borno.
Hukumar yaki da masu yi wa kasa ta'annati (EFCC) ta gayyaci manyan jami'an kamfanin Dangote zuwa Abuja, a cigaba da binciken da take kan badakalar canji.
Ministar jin kai da yaki da fatara, Dakta Betta Edu, ta yi martani kan badakalar cin hancin N3bn a hukumar NSIPA. Ministar ta nesanta kanta daga badakalar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai yi rabon babura ga jami'an tsaro na yan sanda da na yan sandan farin kaya a Kano.
Primate Ayodele ya yi gaggarumin gargadi ga Shugaban kasa Bola Tinubu inda ya bukace shi da ya gaggauta daukar matakan magance matsin tattalin arziki a kasar.
Kungiyar MURIC ta bukaci yan majalisa da su fara rabon buhuhunan shinkafa da sauran kayan abinci da shuka karba daga wajen Shugaban kasa Bola Tinubu.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nusar da mata kan muhimmancin shiga aikin soja musamman nan a sojan kasa. Ya ce an bar su a baya a wurare da dama.
Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC), ta bayyana cewa ta kama wasu mutane da laifin gudanar da ayyukan haramtattun jami’o’i 37 a fadin kasar nan.
Kungiyar yan kasuwa da masu shaguna a masallacin Idi na jihar Kano sun shigar da korafi kan Gwamna Abba da Kwankwaso a wurin kwamishin yan sandan jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari