Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Zai Yi Wani Muhimmin Abu 1 Domin Bunkasa Tsaro a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Zai Yi Wani Muhimmin Abu 1 Domin Bunkasa Tsaro a Kano

  • Jami'an ƴan sanda da na ƴan sandan farin kaya (DSS) da ke a shiyyar Kano ta Arewa za su samu babura
  • Wannan na zuwa ne bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya shirya fara yi musu rabon baburan
  • Rabon baburan dai ya ƙunshi dukkanin ofisoshin jami'an tsaron da ke a shiyyar Kano ta Arewa wacce yake wakilta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai raba babura ga ƴan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke aiki a shiyyar Kano ta Arewa.

Sanarwar hakan ta fito ne daga ofishin mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Shitu Madaki Kunchi, wacce ya bayyanawa manema labarai a jiya, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Sanata Barau zai raba babura ga yan sanda
Sanata Barau zai yi rabon babura ga yan sanda da jami'an DSS a Kano Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Kunchi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba za su fara rabon baburan ga jami'an tsaron na ƴan sanda da na hukumar DSS a shiyyar Kano ta Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a fara rabon?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Tuni muka samu umarni daga mataimakin shugaban majalisar dattawa kan mu fara rabon wanda za mu zagaya duk wasu ofisoshin ƴan sanda da na DSS a Kano ta Arewa. Domin haka muna kira ga duk waɗanda abin ya shafa da su kasance cikin shiri.
"Wannan wata alama ce ta mataimakin shugaban majalisar dattawa na inganta rayuwar jami’an tsaro tare da ƙarfafa musu gwiwa domin yin aiki mai kyau. Daga yanzu za a fara aikin a Kano ta Arewa, daga nan kuma za mu ɗunguma zuwa wasu sassan jihar."

Wannan dai na zuwa ne a cigaba da tallafawa jami’an tsaro a shiyyar Sanatan da yake wakilta inda ya raba motocin Hilux ga ɗaukacin ofisoshin ƴan sanda na ƙananan hukumomin yankin tare da sanya musu wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

Kara karanta wannan

Wasu mata sun fito zanga-zanga a fusace, sun banka wa gidan basarake wuta a Bokkos

Ya kuma bayar da motoci ƙirar Hilux guda biyu ga hedikwatar ƴan sandan jihar.

Barau Ya Raba Motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya raba motoci ƙirar Sharon guda 60 a jihar Kano.

Mutanen da suka ci gajiyar wannan rabon motocin dai sun fito ne daga dukkanin sassan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel