Digirin Bogi Na Kwatano: Tsohon Minista Ya Fadi Dalilin da Yasa Yan Najeriya Ke Tururuwa Zuwa Benin

Digirin Bogi Na Kwatano: Tsohon Minista Ya Fadi Dalilin da Yasa Yan Najeriya Ke Tururuwa Zuwa Benin

  • Tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, ya mayar da martani kan yawaitar takardun digirin bogi daga jami'o'i a Jamhuriyar Benin
  • Adeniran ya ce ƴan Najeriya na gaggawar samun digiri na bogi ne saboda ƙasar nan ta mayar da hankali kan takardun digiri
  • Ya ƙara da cewa waɗannan takardun shaida na bogi da ake samu ta hanyar biyan kuɗi suna lalata tsarin ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, ya ce ƴan Najeriya na zuwa neman digiri na bogi da satifiket a Jamhuriyar Benin da sauran ƙasashe makwabta saboda ƙasar nan na mutunta satifiket ɗin takarda.

Adeniran ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa ya kuma taimaka wajen gaggawar samun takardar shaidar digiri na bogi a ƙasashen.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga har fada sun yi awon gaba da babban basarake

Tunde Adeniran ya yi magana kan digirin bogi
Farfesa Tunde ya fadi dalilin zuwan yan Najeriya Jamhuriyar Benin samo digirin bogi Hoto: @Prof_Adeniran, @Theumar_audu
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar The Punch kan yawaitar takardun digirin bogi daga jami’o’i a jamhuriyar Benin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Cin hancin dake a Najeriya ne waɗannan mutanen suke amfani da shi saboda sun san cewa muna amfani da tsarin da ya gurɓata da cin hanci, hakan ya sanya suke amfani da wannan damar domin cin gajiyar cin hancin dake a ƙasar mu."

Tsohon ministan ya ƙara da cewa yanzu ƴan Najeriya ba su da sha'awar neman ilimi da samun ilimi.

Adeniran ya koka kan yawaitar digirin bogi

Adeniran ya ce batun satifiket ɗin bogi abin takaici ne saboda wasu masu takardun bogi sun shiga cikin ma'aikatun Najeriya.

A kalamansa:

"Sai dai, a ƙasar nan mun fi ba satifiket ɗin takarda muhimmanci. Mutane na zuwa na cewa "abin da muke buƙata shi ne satifiket ɗin makaranta." Da zarar ka samar da shi, magana ta ƙare.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi caraf da likitan bogi mai zubar da juna biyu

"Abin da ake buƙata shi ne a biya ko nawa ne, wanda hakan yana dakusar da ɓangaren ilimi.
"Wannan ne dalilin da ya sa muke da ɗaiɗaikun mutane, waɗanda suke kiran kansu sun gama makaranta waɗanda da ƙyar suke iya haɗa jimla, waɗanda ba za su iya rubuta sakin layi ɗaya na bayani ba. Wannan dalilin da yasa ba mu samun irin cigaban da muke buƙata.
"Waɗannan mutane suna zuwa ne kawai da takardu, kuma, ba shakka, babu ɗayansu da aka haɗa a hukumance."

Ɗan Jarida Ya Faɗi Yadda Ya Samu Digirin Bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan jaridan da ya fallasa yadda ake samun digirin bogi daga Jamhuriyar Benin, ya bayyana yadda ya samo shi.

Umar Shehu Audu ya yi bayanin cewa ko sau ɗaya bai taɓa shiga aji ba, sannan N600k kawai ya kashe ya samu digirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel